Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa zai shiga tsakani domin warware rikicin da ke tsakanin Kamfanin Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG), don tabbatar da zaman lafiya da daidaito a harkar man fetur a ƙasar nan.
Wannan mataki ya biyo bayan taron kwana uku da aka gudanar a Legas, inda ƴan majalisa, da hukumomi da masu ruwa da tsaki a masana’antar suka tattauna kan matsalolin da ke ci gaba da damun sashen mai na ƙasa. Shugaban kwamitin, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin ba zai bari rikici tsakanin manyan masu saka jari da ƙungiyoyin kwadago ya samu tangarɗa ba.
- Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
- Matatar Dangote Ta Dakatar Da Zuwa Ɗaukar Man Fetur, Sai Dai Ka Saya Ta Kai Ma
“Babban burinmu shi ne kawo sauye-sauyen da za su tabbatar da inganci, da adalci da gasa mai kyau ga kowa. Za mu shiga tsakani don tabbatar da cewa babu wani ɓangare da zai ji an tauye masa haƙƙinsa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa kwamitin ya damu da matsalolin samar da ɗanyen mai da ke kawo cikas ga masana’antar.
Haka kuma, taron ya sake nazarin ce-ce-ku-ce kan yadda Kamfanin NNPC Limited ya karɓi kadarorin OVH Energy. Ugochinyere ya tabbatar da cewa bincike na musamman kan wannan ciniki ya kai matakin ƙarshe, wanda ya bambanta da binciken farko da aka yi watsi da shi a zauren majalisar. Duk da cewa wasu masu ruwa da tsaki ba su miƙa takardunsu ba, ya ce kwamitin zai ci gaba da aikinsa domin cika alƙawarin majalisar.
Ƴan majalisa sun yaba da ƙoƙarin Hukumar NMDPRA, da tashar Tace Mai ta Dangote, da sauran masu zuba jari a fannin, tare da lura da cigaba da ake samu wajen gyaran tashar tace mai ta Fatakwal. Rahotannin ƙananan kwamitoci da aka kafa a taron za su fito nan gaba kaɗan, kuma za su zama tubalin dokokin majalisa kan rabon ɗanyen mai, da sabunta matatun mai da kuma inganta tsarin sa ido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp