Khalid Idris Doya" />

Makon Likitoci: NMDA Ta Bayar Da Kiwon Lafiya Kyauta Ga Mutane 500 A Bauchi

Sama da mutanen kauyen Dugulbi su dari biyar, maza da mata, yara da kanana ne suka ci gajiyar duba lafiyarsu kyauta, hadi da basu magunguna daga kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Bauchi.

Aikin jinyar wanda aka gudanar a jiya Laraba a cikin bikin makon likitoci wanda aka gudanar a jihar Bauchi, kungiyar ta samar da kwararrun likitocin da suka sadaukar da lokacinsu hadi da bayar da kula da lafiya ga jama’an kauyen na wuni guda kyauta.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a wajen aikin, shugaban kungiyar, Nigeria Medical Doctors Association reshen jihar Bauchi, Dakta Lamaran Dattijo ya shaida cewar sun yi wannan aikin ne domin raya bikin makon tunawa da aikace-aikacen likitoci a Nijeriya.

Ya shaida cewar taken taron na bana shine; ‘kai aikin lafiya ga kowa da kowa; ba tare da la’akari da inda yake, yana gari ne ko yana kauye, yana da kudi ko baida shi,’ kamar yadda ya shaida

Dakta Lamaran Dattijo ya ci gaba da bayyanin yadda suka aiwatar da aikin a kauyen na Dungulbi, yana mai bayanin cewar sun zabi kauyen ne domin tabbatar da an kai kula da jinya ga kowa da kowa, “mun zabi Dungulbi domin gudanar da wannan aikin jinya kyauta ne la’akarin da muka yi na cewa ita wannan kauyen duk da tana kusa da cikin garin Bauchi amma lallai suna fama da matsalar rashin asibiti karami ko babba, sannan mun lura akwai jama’a da dama a wannan kauyen,”

Ya shaida cewar a don haka su suka kwaso jiki hade da sauran kwararrun likitoci daga sashi daban-daban da suka kushi likitocin ido, kwakwalwa, da sauran likitocin da suka samar duk aiwatar aikin jinyar.

Ya bayyana ababen da suka aiwatar don kula da lafiyar jama’a, “mun auna tsayin yaran kauyen sabili da nauyi da tsayi shine ke nuna yaro na girma yadda ya kamata ko ba yadda ya kamata ba, sannan sai mu baiwa iyaye shawarorin da suka dace su bi, bayan nan mun baiwa yara maganin tsotsar ciki wanda yana daga cikin abun da ke hana yaro girma.

“Sauran jama’a kuma mun duba jama’a kan fannonin cututtukan yau da kullum kamar su Amai da gudawa, ciwon baya, olsa, ciwon hawan jini, ciwon suga, haka nan mun zo da likitocin ido dukka kowani bangare mun duba jama’a kana mun basu magunguna kyauta,” Inji Dakta Lamaran

Ya bayyana cewar wadanda cututtukarsu suka yi kamari da ba za su iya basu kulawar likita a wuni gudan ba, sun tsara yadda za su dauki sunayensu da kuma basu damar halartar babban asibitin jihar Bauchi domin su samu kulawar likitocin kamar yadda suka rigaya suka yi niyya albarkacin wannan rana mai muhimmanci a garesu.

Shugaban kungiyar na NMDA, ya kuma shaida cewar bayan da suka duba lafiyar jama’an, sun kuma basu magunguna kyauta hadi da raba musu gidajen sauro domin kariyan kai daga cutar maleriya.

Da yake bayanin godiya a madadin jama’an kauyen, Sarkin Dungulbi, Malam Musa Gambo ya nuna gayar godiyarsu ga kungiyar likitoci na jihar Bauchi a bisa zabin kauyensu a matsayin wajen da za su aiwatar da wannan aikin jinkai a garesu, ya yi fatan alkairi ga kungiyar.

Da ya juya kan halin da kauyen ke ciki kuwa, Sarkin ya shaida cewar sama da shekara 100 wannan kauyen kenan, inda ya shaida cewar yaruka daban-daban musulmai da kirista ne suke rayuwa a wannan kauyen amma suna fuskantar matsalar rashin samun ababen more rayuwa, inda ya tabbatar da cewar suna da yawan jama’a dubbai a kauyen amma har zuwa yau basu da asibiti ko daya, ya shaida cewar ba su da wasu ababen more rayuwa duk da kasancewarsu kauye mafi kusa da cikin garin Bauchi.

Sarkin ya shaida cewar suna da yara sama da dubu da suke karatu a firamare mai aji biyu, wanda ya shaida cewar hakan na kasance musu matsala ta fuskacin ilimin ‘ya’yansu, ya nemi gwamnati da su duba kauyen da idon rahama.

Wasu daga cikin ‘ya’ya matan da suka ci gajiyar duba lafiya kyauta da su da ‘ya’yansu, Lydia Solomon da kuma Hajara Yakubu sun nuna farin cikinsu a bisa cin gajiyar shirin, inda suka bayyana cewar a dukkanin lokacin da nakuda na haihuwa ya riskesu suna gayar shan azaba wajen zuwa asibiti kasantuwar basu da koda babban shagon magani a kauyen, “sai mun je cikin garin Bauchi ko Inkil muke samun wurin da za mu haihu idan haihuwa ta zo dole sai an je asibiti, don haka muna shan wuya ta wannan jabinin,” Inji su

Da yake bayani, shugaban matasan kauyen na Dungulbi, Musa Muhammad Na’ibi, ya nuna takaicinsa kan rashin ababen more rayuwa da kauyen ke fama da shi, “dukkanin inda ake son kauye ta kai nan kauyen ta kai, muna da dumbin jama’a da suke rayuwa a cikinta amma ba mu da ababen more rayuwa, hatta asibiti babu, babu makarantu babu komai na jin dadin rayuwa. Babban abun takaici ma shi; wannan kauyen nisanta kilomita shida 6 ne kacal daga cikin garin Bauchi amma a ce ba mu da ababen more rayuwa. Wannan kauyen tana kusa da jikin makabartan Bauchi ne, ko don makabartar da kenan ya dace mu ci gajiyar samar mana da ababen more rayuwa domin masu biso suke samun saukin tafiyar da lamari,” Inji shi

Daga bisani shugaban matasan ya yi kira da babban murya ga gwamnatoci da su kai musu dauki na ababen more rayuwa, inda ya shaida cewar al’adu da daman gaske ne suke rayuwa a wannan kauyen ba tare da nuna banbancin kabilanci ko addini ba.

Exit mobile version