A ranar Litinin dinnan aka fara gabatar da wani taron kasa da kasa mai taken “Gina Gada tsakanin Mazhabobin Musulunci da Kungiyoyin Musulunci” a birnin Makkah na kasar Saudaiyya.
Taron wanda kungiyar kasashen musulmi ta duniya MWL ta shirya kuma Sarki Salman bin Abdulaziz ya dauki nauyin taron, ya samu halartar wakilai da dama na mabiya addinin Islama. Malamai sun bayyana aniyarsu ta inganta al’amura gama gari don farfado da gudummawar da al’ummar Musulmi ke bayarwa wajen wayar da kai da samar da ci gaba.
- Sakamakon Taron Kasashen Musulmi Da Larabawa: Saudiyya Da Nijeriya Za Su Jagoranci ‘Yantar Da Falasdin
- Samar Da Jami’ar Musulunci A Jihar Kaduna Alheri Ne – Bola Ige
Shugaban kungiyar MWL, Mohammed Al-Issa l, ya sanar da shirin kaddamar da daftarin aiki da ke bayyana muhimman ka’idojin samar da hadin kai a tsakanin kungiyoyin Musulunci don tunkarar kalubale yadda ya kamata.
Al-Issa ya kuma bayyana irin farin cikinsa da karbar bakuncin taron mai dimbin tarihi a Makkah tare da jaddada bukatar hadin kan al’ummar Musulmi.
Al-Issa ya yi gargadi game da kalaman bangaranci, ya kuma yi kira da a rika yada labaran da suka dace a kafafen yada labarai da ke kara samar da hadin kai. Daga nan sai ya mika godiyarsa ga mahukuntan kasar Saudiyya kan goyon bayan da suke ba shi, ya kuma yi addu’ar Allah ya kara masa lafiya.
An fara taron ya samu kyakkyawar tarba daga babban Mufti na Saudiyya, Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh, wanda Dr. Fahd Al-Majid ya gabatar.
Al-Sheikh ya jaddada muhimmancin hadin kai a Musulunci, ya kuma yi gargadi kan illar rarrabuwar kawuna tare da bayyana irin rawar da malamai ke takawa wajen samar da hadin kai a tsakanin musulmi.
Ya godewa mai kula da masallatai masu alfarma guda biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz kan goyon bayan taron tare da yabawa kokarin hadin kan musulmi, karkashin jagorancin Yarima Mohammed bin Salman, Yarima mai jiran gado kuma Firayim Ministan Saudiyya.
An mika godiya ga wadanda suka shirya taron, wanda MWL ya wakilta, saboda hidimar da suke ci gaba da yi wa Musulunci da Musulmai.
Hissein Brahim Taha, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC, ya yabawa sarki Salman da yarima mai jiran gado Mohammed bisa goyon bayan taron.
Ya yi bayani cewa muhimmin taron zai inganta hadin kai a tsakanin mazhabobin Musulunci, tare da shawarwarin da za a yi amfani da su wajen samar da hadin kai da magance sabani.
Taha ya kuma yabawa kungiyar MWL bisa sadaukarwar da take yi wa Musulunci da Musulmin duniya.
A gefe guda kuma, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin MWL da OIC kan hadin kai a tsakanin Kungiyoyin biyu.
An rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Cibiyar Fiqhu ta Musulunci ta MWL da Cibiyar Nazarin Fiqhu ta kasa da kasa ta OIC don bunkasa hadin guiwa a fannin bincike.