Wani malami a wata makaranta a garin Huai’an da ke lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, ya samu karbuwa sosai a yanar gizo bayan wani bidiyo da aka yada shi yana sanya rayuwarsa cikin hadari don ceton wani yaro da ya yi kokarin fadowa daga saman bene a hawa na shida.
Yaron dan shekara 12 daga Huai’an an bar shi shi kadai a cikin gidan kuma ya tafi baranda don shigo da wasu mayafai, lokacin da ya zame ya fadi babu abin da ya rike shi sai wani stumman tufafi daga rataye a wajen benen.
Ba da dadewa ba wani makwabcin kasa, wanda ake kira Hou ya lura da shi, wanda nan da nan ya gudu zuwa daidai wannan wuri a saman inda yake. Hou ya kama karfen jikin taga da hannu daya, ya rataye jikinsa ta tagar don ya rike yaron na kusan mintuna 20 har sai da ‘yan kwana-kwana suka zo.
Daga baya Hou ya fada wa kafofin yada labarai cewa shi malami ne a makarantar koyon harsunan waje. Ya ce, “Hannaye na duka sun sage gaba daya bayan na rike yaron na tsawon lokaci da hannu daya, amma da yake na san cewa rai nake rike da shi a hanuna, ban yi tunanin sakewa ba.”