Rahoton zango na biyu shekarar 2024 kan tattalin arziki da Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar ya nuna cewa, Man da ake shigowa da shi cikin kasar, ya ragu da kashi 35, wanda kuma ya kai yawan dala biliyan 2.79, daga dala biliyan 4.31 a zango baya.
Wannan raguwar ta kara bunkasa fannin mai da iskar Gas na kasar, duk da ci gaba da garanbawul da ake yi a kan bangaren tattalin arzikin kasar, biyo bayan cire tallafin mai da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.
- Rashin Wutar Lantarki A Arewa Zai Dauki Tsawon Lokacin Kafin Ya Gyaru – Rahoto
- Katsewar Lantarki: Masu Masana’antu Sun Kashe Naira Biliyan 238.3 Wajen Samun Wuta
Kazalika, rahoton ya yi nuni da cewa, kayan da ake shigowa da su cikin kasar, sun ragu da kashi 20.59 wanda kudinsu ya kai dala biliyan 8.64 daga dala biliyan 10.88, da aka samu a zango na daya, a 2024.
Bisa fashin bakin da aka yi, ya nuna cewa, raguwar ta shigo da man, ya ragu zuwa dala biliyan 2.79 daga dala biliyan 4.31 a zango na gaba.
Bugu da kari, a fannanin da bai shafi mai ba kuwa, an samu raguwar dala bliyan 5.85 daga dala biliyan 6.57, a zango na gaba.
A kan fashin bakin jimlar kayan da aka shigo da su cikin kasar, ta nuna cewa, an samu raguwr kashi 67.72.
Rahoton ya ci gaba da cewa, dagewar da aka yi wajen hako danyen mai a kasar, ya ragu da kashi 4.51 zuwa Gangunan danyen mai miliyan 1.27, ya ragu a zango na biyu na 2024 da ake hakowa a kullum.
Sai dai, rahoton ya sanar da cewa, yawan samun satar danyane mai da lalata bututun mai da wasu bata gari ke yi a yankin Niger Delta, an ci gaba da zamowa kalubaale, wajen samar da man a kasar.
Wannan dai, na faruwa ne, saboda yawan satar danyen mai da kuma lalata butun mai, wanda hakan ya janyo aka samu raguwar man samfarin Forcados, Bonny, Kua-Iboe, Escrabos da Brass streams.
Duk wannan koma bayar da aka samu farashin na dayen mai ya dan ragu, a kasuwar duniya.
Sai dai, danyen main a Nijeriya samfarin Bonny Light, farashin Gangarsa ya karu zuwa dala 86.97 akan kowacce Ganga daya a zango na biyu na 2024, wanda ya hakan ya samar da dan sauki, ga kudaden da ake kashewa wajen shigo da man
Fitar da danyen man da iskar Ga da sun kai kashi 87.38 wanda hakan ya nun jimlar kara samun kudaden shiga a cikin wannan zangon, hakan ya kuma samar da sauki na raguwar dala biliyan 12.18 daga dala biliyan 12.42 zangon farko na 2024.
Tun da farko, Jaridar PUNCH ta ruwaito rahton na CBN da ya fitar, an samu jimlar raguwar dala biliyan 2.97, a fannin mai da ake shigo da shi da kuma sauran wasu kaya.