Manchester City ta koma mataki na uku a teburin gasar Firimiya bayan buga canjaras da abokiyar karawarta Tottenham a filin wasa na Etihad da ci 3-3 a ranar Lahadi.
Guardiola ya yi tunanin kwallon da Grealish ya zura a minti na 81 ne zai tabbatar wa kungiyar samun maki 3, amma Kulusevski ya farke a minti na 90 wanda hakan yasa City ta buga kunnen doki na uku a jere a gasar.
Kuma hakan yasa mai jan ragamar Firimiya ta bana Arsenal ta baiwa City maki uku rigis.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp