Manchester Na Magana Da Leceister City Domin Sayen Maddison

 kungiyar  kwallon  kafa ta Manchester United tana kan gaba wajen siyan dan wasan tsakiyar Leceister City, James Maddison, bayan da wasu rahotanni suka bayyana cewa tuni Magana tayi nisa tsakanin  kungiyoyin biyu.

 kungiyoyin Arsenal da Tottenham da Manchester City dai sun nemi dan wasan a kwanakin baya wanda hakan yaja hankalin Manchester United ta shiga zawarcin dan wasan wanda ya zura  kwallaye bakwai ya taimaka aka zura  kwallaye bakwai a kakar wasan data gabata.

Rahotanni dai sun bayyana cewa  kungiyar  kwallon  kafa ta Manchester United ta bayyana wa dan wasan cewa zata bashi fam miliyan bakwai a duk shekara matakin da ake ganin abune mai wahala dan wasan ya ki amincewa da tayin.

Maddison dai yana da ragowar kwantaragin shekara uku a  kungiyar wanda hakan yasa Leceister City tace dole sai United ta biya fam milyan 60 idan har tana son siyan dan wasan tsakiyar.

Sabon kociyan  kungiyar ta Leceister City, Brendan Rodgers ya bayyana cewa baya fatan  kungiyar ta rabu da Maddison sai dai ya bayyana cewa yakamata a siyar da dan wasan da tsada idan ya zama dole sai an siyar dashi domin su samu kudin siyan wani dan wasan.

Maddison dai ya koma Leceister City daga  kungiyar Norwich kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da tauraruwarsu ta haska a kakar wasan data gabata kuma tuni kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer ya bayyana cewa zai siyi matasan ‘yan wasa a bana domin dawo da martabar  kungiyar wadda ta kammala kakar wasa ta bana a mataki na shida.

Exit mobile version