Manchester United ta kammala siyan dan wasan gaban Denmark, Rasmus Hojlund daga Atalanta kan fan miliyan 72.
Dan wasan mai shekaru 20, wanda ya koma kungiyar ta Serie A a shekarar 2022 kuma ya zura kwallaye 10 a wasanni 34 da ya buga a bara, ya koma Old Trafford kan kwantiragin shekaru biyar.
- Barnar Da Cutar Diptheria Ke Ci Gaba Da Yi A Jihohi 7 Da Abuja
- Na Fi So Na Fito A Masifaffiya -Amina Miloniya
“Na kasance masoyin wannan babbar kungiya tun ina karami,” in ji Hojlund.
“Na yi mafarkin shiga Old Trafford a matsayin dan wasan Manchester United.”
Shi ne dan wasa na uku da kocin United Erik Ten Hag ya dauko a bazara bayan Mason Mount daga Chelsea kan fan miliyan 55 sannan golan Inter Milan Andre Onana ya zo kan fan miliyan 47.2 daga Inter Milan.
Zakarun Ligue 1, Paris St-Germain, kuma rahotanni sun ce suna zawarcin Hojlund a matsayin wanda zai maye gurbin Kylian Mbappe.
Hojlund ba zai buga makonnin farko na kakar wasa ta 2023-24, wanda United za ta fara da Wolves ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, bayan da ya samu rauni a lokacin atisayen tunkarar kakar wasa da Atalanta.