Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Manchester United Za Ta Sayar Da Pogba A Karshen Kakar Wasa

by Abba Ibrahim Wada
January 4, 2021
in WASANNI
2 min read
Pogba
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta shirya sayar da dan wasa Paul Pogba a karshen kakar wasa idan har aka samu kungiyar da za ta iya biyan abinda kungiyar ta saka akansa.

A ranar Juma’a ne mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa, dan wasa Paul Pogba ya kama da wuta kuma yana daya daga cikin wadanda za su kai kungiyar inda suke fata a wannan kakar.

samndaads

Solkjaer ya tabbatar da hakan ne a daren Juma’a bayan da dan wasan ya zama dan wasan da ya fi nuna bajinta a fafatawar da kungiyar ta samu nasara da ci 2-1 akan kungiyar Aston Billa kuma nasarar da ta sa yanzu kungiyar ta ke maki daya da Liverpool wadda za ta buga wasa da Southamton idan an jima.

A kwanakin baya ne wakilin dan wasa Pogba kuma mai kula da harkokin wasanninsa, Mino Rioala, ya bayyana cewa, Pogba ba ya jin dadin wasa a Manchester United ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu lamarin da ya haifar da cece-kuce kuma wasu suke ganin da amincewar Pogba wakilin nasa yayi wannan maganar.

Amma Pogba, wanda ya sake koma wa Manchester United daga Juventus a shekarar 2016, bai boye aniyarsa ta buga wasa a Real Madrid nan gaba ba kuma a watan Nuwamban da ya gabata kociyan tawagar Faransa, Didier Deschamps, ya sanar cewa, Pogba ba zai taba samun farin ciki a United ba a lokacin da kungiyar ba ta samun nasara a wasanni. Sai dai yanzu abubuwa sun fara canja a nasarar kungiyar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shin Neymar Da Mbappe Za Su Bawa Pochettino Hadin Kai?

Next Post

Pochettino: Tsohon Dan Wasa Yanzu Kuma Kociyan PSG

RelatedPosts

Lampard

Ana Dab Da Korar Lampard A Chelsea

by Abba Ibrahim Wada
22 hours ago
0

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugabannin kungiyar ta...

Dele

Cinikin Dele Alli: PSG Ta Fara Magana Da Tottenham

by Abba Ibrahim Wada
22 hours ago
0

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Dele...

Copa

Gasar Copa Del Rey: Real Madrid Ta Yi Abin Kunya

by Abba Ibrahim Wada
22 hours ago
0

Real Madrid  ta buga gasar cin kofin Copa del Rey...

Next Post
Pochettino: Tsohon Dan Wasa Yanzu Kuma Kociyan PSG

Pochettino: Tsohon Dan Wasa Yanzu Kuma Kociyan PSG

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version