Gidauniyar hamsakin dan kasuwar nan, Dahiru Barau Mangal ta dauki nauyin yi wa masu ciwon mafitsara fiye da 80 aikin tiyata a Jihar Katsina.
Wani mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, Hussaini Kabir ne, ya bayyana hakan a yayin gudanar da atisayen a asibitin kashi na Amadi Rimi da ke Katsina a ranar Talata.
- An Dakatar Da Jami’in Hukumar NIS Saboda Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi
- Sakataren Gwamnati Da Ministoci Na Ganawar Sirri Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
Ya bayyana cewa an dade ana gudanar da irin wannan aiki kyauta, musamman a kowane zangon wata uku na shekara, domin gidauniyar ta ware kudade don yin hakan.
Kabir, ya ce wasu daga cikin cututtukan da gidauniyar ke daukar nauyin jinyarsu a kashi na uku na shekara, sun hada da ciwon kaba da sauransu ga majinyata wadanda galibinsu masu rauni ne.
A cewarsa, ana ci gaba da aikin tantance marasa lafiya da su ke da kananan cututtuka, inda ya bayyana cewa za a yi wa wadanda ke da kananan matsaloli magani, a ba su magunguna kyauta a kuma sallame su.