Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazan Jihar Kano (NAHCON), Farfesa Imamu Sale Pakistan ya bayyana cewa maniyyata 700 wadanda aka bari a bara za su fara tashi a jirgin farko a Jihar Kano.
Jihar Kano ta samu gurbin maniyyata guda 552 a Hajjin 2023 daga shalkwatan hukumar da ke Abuja, wanda ya kusan ninka adadin wadanda suka sauke farali a bara daga Jihar Kano.
Ya ce wannan abun farin ciki ne da kuma godiya ga Allah Madaukakin Sarki da wannan ni’ima tasa.
Farfesa Pakistan ya bayana haka ne lokacin bikin bude bitar da ake shirya wa maniyyata na Jihar Kano a duk shekara, wanda ya samu halatar daukacin masu ruwa da tsaki a kan gudanar da aikin hajji mai inganci da aka yi a dakin taro na makarantar nazarin harshen labarci da ke Kano a karshen makon nan da ya gabata.
Babban sakataran hukumar NAHCON na Jihar Kano, Alhaji Abba Dambatta ya ce su dai alhazai ko maniyyata bakin Allah ne kuma lallai su tsaya su natsu su koyi duk abin da ake karantar da su a bitar nan domin ta haka ne za a samu aikin hajji mai inganci kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya yi umarnin a yi.
Haka kuma ya yaba wa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan hadin kai da gudumawa da ke bai wa hukumar.