Takin zamani na gwamnatin tarayya mai lamba 20:10:10, ta kayyade farashinsa a kan naira 5,500, amma a yanzu, farashinsa ya kai sama da naira 14,000 wanda kuma ba dukkan manoma ke iya saye ba.
A kalla a cikin wata shida da suma wuce, farashin takin zamani na ci gaba da tashin gwaron Zabi, inda hakan ya janyo manoma a fadin kasar nan, ke ci gaba da koka wa.
A watan Janairun 2022 an sayar da buhun takin daya, daga naira 11,000 zuwa naira 16,000 amma a yanzu, ana sayar da buhu daya daga naira 24,000 zuwa naira 30,000, amma ya danganta da irin nau’insa ko kuma gurin da ake sayar da shi.
Ko da yake, matsalar ba Nijeriya kadai ta shafa ba, abu ne da ya shafi kusan duniya baki daya amma a Nijeriya matsalar har ta kai wasu daga cikin manoma bango.
A yankun da dama a Nijeriya manoma ba sa iya yin noma ba tare da yin amfani da takin ba, musamman a inda ba a samun kasar noma mai inganci.
Ci gaba tashin farashin ya tilasta manoma da dama wajen yin amfani da takin gargajiya.
Ratotanni daga sassan Nijeriya sun nuna cewa, farashinsa na ci gaba da tashi, inda ake ganin zai ci gaba da tashi a watanni masu zuwa.
A garin Abuja da kewaye da jihohin Neja da Nasarawa.
Nau’in Indorama da Dangote da Notore su ne ake sayar wa daga naira 19,000 zuwa naira 25,000.
NPK, musamman 15:15:15 farashin buhu daya mai nauyin kilogiram 50, ya kai naira 30,000, wannan ya danganta da irin nau’insa.
Binciken da aka gudanar a jihar Kano, ya nuna cewa, farashin nau’insa samfarin Indorama a yanzu ya kai naira 22,000, sabanin farashin naira 12,000 da aka sayar a 2021,inda samfarin Dangote a yanzu, ya kai naira N19,000 sabanin naira 9,000 a 2021, haka kuma farashin samfarin Waraka, a yanzu ana sayar da shi a kan naira 25,000 sabanin naira 16,000 a 2021. Bugu da kari, samfarinsa na NPK 15:15:15 wato na Nagari a yanzu ana sayar da shi a kan naira 24,500 sabanin N12,000, NPK 20:10;10 a 2021, inda samfarin Golden Penny a yanzu ana sayar da shi a kan naira 25,000 sabanin naira 13,000 NPK 20:10:10 na Kasco a yanzu ana sayar da shi a kan naira N15,000 sabanin naira 9,500.
Malam Danladi Balarabe, manomi a karamar hukumar Bagwai a ya ce, tsadar Takin zamani ya sa manoma da dama a yankin rugumar yin amfani da takin gargajiya kuma noman bana, ba dukkan manomi zai iya sayen Takin zamanin ba.
Shi ma wani manomi a karamar hukumar Kiru Muhammad Tahir ya ce, wasu manoma a yankin na tunanin fara yin amfani da wani sabon sanadarin Ruwa na takin zamani da wani kamfani ya gabatar wa manoma a yankin a matsayin takin zamani wanda kuma yana da saukin farashin.
A jihar Neja, manoma da dama sun koma yin amfani da bola a matsayin taki, inda wani manomi Mohammad Umar ya ce, tuni ya koma yin amfani Bola wajen noma Masara da Shinkafa saboda tsadar farashin takin zamani.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gano manoma na ainahi domin ta taimaka masu, musamman da takin zamani da kuma samar masu da kayan aikin noma a farashi mai sauki.
Adamu Aliyu, wani manomi a karamar hukumar Kacha a jihar ya sanar da cewa, yana yin amfani da kashin kaji ne a gonarsa domin farashin takin zamani a jihar ya yi tsada, inda ya kara da cewa, a baya yana sayen buhu daya na kashin kajin mai nauyin kilogirkm 100 kan naira 2,500 wanda shi ma farashin sa, ya kara tashi sama.
Shi ma wani manomi a karamar hukumar Gbako Muhammad Muhammad ya bayyana cewa, yin amfani da bola wajen yin noman ya fi masa sauki kan yin amfani da takin zamani, musamman saboda tsadarsa, inda ya kara da cewa, idan kana da naira 10,000 zaka iya yin hayar mota kirar pickup ta kwaso maka bola ta kai maka Gona maimakon sayen buhun takin zamani kan daga naira 22,000 ko kuma a kan naira 25,000.
Wani mai kiwon Kajin gisan Gona Suleiman Mohammed, ya tabbatar da cewa, suna sayar da buhu daya na takin kashin kaji mai nauyin kilogiram 100 a kan farashin naira 3,000.
Suleiman Mohammed ya kara da cewa, bukatarsa na kara yawa matuka, musamman ganin ana kara samun manoma da ke bukata a tanadar masu da kashin domin ba za ka kawai zo, kace kana bukata ka kuma samu a nan take ba manoman na biyan kudaden su ne da wuri, don a tara masu Kashin Kajin.
A cewar Suleiman Mohammed, wasu mutane sun rungumi sana’ar sayen Kashin Kajin domin su sayar wa da manoma.
“Bukatarsa na kara karuwa matuka, musamman ganin ana kara samun manoma da ke bukata a tanadar masu da kashin domin ba za ka kawai zo, ka ce kana bukata ka kuma samu a nan take ba manoman na biyan kudaden su ne da wuri, don a tara masu Kashin Kajin”.
A jihar Filato wasu manoma kamar su, John Ajiji na ci gaba da kokawa kan tashin farashin na Takin zamani a jihar inda suka bayyana cewa, tsadar farashin na Takin zamani, ya yi matukar janyo masu koma baya wajen gudanar da aikin noma, inda kuma hakan ya sa suke fuskantar wahala da ban da ban a fannin.
Ajiji wanda manomi ne a Jos ta Arewa Maso Gabas ya sanar da cewa, tsadar farashin na takin zamani ya sa ya rage yawan noman da yake yi domin bai da karfin da zai iya sayen takin zamani a kakar noamn bana.
Ya ci gaba da cewa, a baya a kowacce damina, ya na sayen Takin zamani Buhu 10 domin yin noma, amma a yanzu, ko buhu biyar ba zai iya saye ba.
Ajiji ya kara da cewa, a yanzu suna sayen takin zamani samfarin NPK Buhu daya a kan naira 28,000, inda kuma suke sayen buhu daya samfarin Urea a kan naira 21,000.
“A baya ako wacce damina, ya na sayen takin zamani buhu 10 domin yin noma, amma a yanzu, ko buhu biyar ba zai iya saye ba”.
A cewar John Ajiji, idan har ya na bukatar ya sayi Takin zamani mai yawa don yin amfani da shi a Ginarsa a yanzu sai in ya kashe sama da naira 100,000 zai iya saye.
“Idan har ya na bukatar ya sayi Takin zamani mai yawa don yin amfani da shi a Ginarsa a yanzu sai in ya kashe sama da naira 100,000 zai iya saye”.
John Ajiji ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da wadataccen Takin zamani ga manoman da ke kasar nan musamman kananan manoma.
” Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wadataccen takin zamani ga manoman da ke kasar nan musamman kananan manoma, musamman idan aka yi la’akari da kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi na wadata kasar nan da abinci mai ya wanda zai kuma kai ga ana fitar da shi zuwa sauran kasuwannin duniya domin sayar wa”.