Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Gwari, Hon. Bashir Zubairu Birnin Gwari (Chiroma), ya ce manoma sun yi asarar sama da naira miliyan 100, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a gonakin masara a karamar hukumar.
Dan majalisar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da gidan rediyon BBC Hausa a ranar Laraba kan harin da ‘yan bindiga suka kai gonakin masara da ke Kwaga da Unguwar Zoko a karamar hukumar Birnin Gwari a ranar Lahadi.
- Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci
- Mata A Dage Da Karatu Yin Haka Taimakon Kanku Ne Da ‘Ya’yanku – Zainab Ahmad
Ya ce idan har gwamnati ta gaza magance irin wannan ta’asa, to jama’a ba su da wani zabi illa su kare kansu.
“Asara ce babba ta sama da naira miliyan 100, kuma su ’yan bindiga ba za su daina ba, domin wani abu ne da suka yi watanni biyu zuwa uku da suka wuce. Suna ikirarin cewa an kai wa mutanensu hari, an lalata musu dukiyoyi, kuma dole ne a mayar musu da makamansu da aka kwace,” in ji shi.
Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai a gonar masara a ranar Lahadin da ta gabata ya faru ne kasa da sa’o’i 48 bayan shugabannin addini da na al’umma sun gana da shugabannin ‘yan bindiga a yankin, inda suka tattauna batun zaman lafiya.
Dangane da yarjejeniyar zaman lafiya da ake cimma, dan majalisar ya ce mutanen kauyukan da abin ya shafa da suka yi asarar dukiyoyinsu da ‘yan uwa a sakamakon hare-haren ya kamata a biya su diyya kan asarar da suka yi.
“Ba zai yiwu a zauna da ’yan bindiga a cikin yarjejeniyar zaman lafiya ba, daga baya a ba su makudan kudade, baya ga dukiyar da suka kwace daga hannun mutanen kauyukan da ba su ji ba ba su gani ba, mutanen da suka kashe, da dukiyoyin da suka lalata. Ka yi tunanin irin mummunar asarar da aka yi wa manoma, amma duk da haka kuna son a samu yarjejeniyar zaman lafiya da su.
“A kan wannan yarjejeniyar zaman lafiya, ina so in yi kira ga shugabanni daga gwamnatin tarayya da su sani cewa wani bangare na yarjejeniyar ya kamata ya hada da biyan diyya ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da aka lalatar da kayayyakin gonakinsu,” in ji shi.
Chiroma ya kara da cewa, a baya, a wata yarjejeniyar zaman lafiya, an gayyaci wasu shugabannin ‘yan bindiga zuwa fadar Sarkin Birnin Gwari, kuma an ba su makudan kudade a cikin yarjejeniyar zaman lafiya.
“A halin da ake ciki, talakawan da aka sace iyalansu da aka lalatar da rayuwarsu ba su samu komai ba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da ba wa fararen hula makamai ba shi ne mafita ba, amma idan lamarin ya ta’azzara, mazauna yankin za su yi wa kansu mafita.
Ya kuma koka da yadda ake damke mutanensa masu sayan makamai domin kare kansu, inda ya ba da misali da wasu mazauna Kutemeshi da aka kama aka tsare su a ofishin ‘yansanda a watan jiya.