Masana lafiyar kwakwalwa sun ce yawan mantuwa na taka rawa wajen samun zuciya mai sauki, kamar yadda Charan Ranganath wani masanin lafiyar kwakwalwa ya rubuta a cikin wani sabon littafinsa.
Masanin ya ce dalilin da ya sa kwakwalwa ke tuna abin da ya wuce, yana da alaka da yadda mutum ke kallon kansa da kuma sauran mutane da yadda duniya take.
- APP Ta Lashe Kujeru 22 A Zaben Kananan Hukumomin Ribas
- Sin Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaron MDD Da Kada Ya Yi Watsi Da Bincike Game Da Fashewar Bututun Gas Na Nord Stream
Farfesa Ranganath, wanda ya kwashe shekara talatin yana karantar da halayyar Dan’adam da yadda Dan’adam ke tunani tare da hanyoyin tuna abin da ya wuce da mantuwa, ya ce yawancin bayanan da ake bayarwa kan mantuwa ba haka suke ba, saboda mantuwa na bayar da gudummawa cikin rayuwar muyane.
Masanin lafiyar kwakwalwar ya tattauna da Dabid Robson, dan jarida a fannin kimiyya, kan yadda mutane za su fahimci kwakwalwarsu domin samun kwanciyar hankali.
Dan’adam na iya ajiye abu a kwakwalwarsa da taimakon sauye-sauyen da ake samu na alakar da ke tsakanin kwayoyin da ke isar da sako, ka’idar koyo bisa kuskure ita ce, lokacin da kuke kokarin tuno abubuwan da suka wuce, kwakwalwa na fitar da abubuwa masu kyau tare da kokarin tauye wadanda ba su da kyau ta hanyar alakanta bayanan da na gaskiya.
Wannan yana nufin cewa hanya mafi kyau don karin koyo ita ce mutum ya kalubalanci kansa domin nemo abubuwan da muke son koyo, saboda ta haka ne mutum zai gane inda kwakwalwarsa ke da rauni, kuma hakan zai kara taimaka wa kwakwalwa wajen tuna abubuwan da suka faru.
Shi ya sa a ko da yaushe ana son mutum ya rika kokarin sanin wani abu, kamar misali, idan za ka je wani wuri da ba ka sani ba, maimakon ka yi amfani da manhajar Google, sai mutum ya yi amfani da kwakwalwarsa ko ta hanyar tambaya domin gano wurin, hakan na da matukar tasiri.
“Matsalar ita ce, yayin da muke girma, shekaru na kama mu, ba lalle ba ne a ce ba ma iya haddace abubuwa, illa dai a ce ba ma mayar da hankali a kan bayanan da ya kamata mu tuna.
“Abubuwa na dauke mana hankali, kuma dukkanin wadannan abubuwa da ba su da muhimmanci, suna dauke mana hankali maimakon mu bayar da muhimmanci ga abubuwan da ke da amfani garemu.
“Saboda haka idan muka bukaci tuna wadannan abubuwa, sai mu kasa samun bayanin da muke nema.
“Masanin ya ba da shawarori na yadda za su taimama. Ta farko, ita ce abu ya kasance fitacce na daban. Abubuwan da muke sanya wa kwakwalwarmu suna gogayya ne da juna, saboda haka duk abin da ka fi yawan amfani ko ambato zai fi zama a kwakwalwarka.
“Bayanan da ke kwakwalwarmu masu alaka da wasu hotuna na daban ko na musamman da sauti da ji a jika, su ne wadanda suke zama a kwakwalwarmu.
“Mayar da hankali kan bayanai masu muhimmanci da jikinmu ya ji ko ya san su, maimakon haddace su, ya fi taimaka mana haddace abubuwa.
“Dabara ta biyu ita ce, mutum ya mayar da hankali wajen tsara abubuwa a kwakwalwarsa, domin ya ba su ma’ana sosai. A littafin, ya tattauna kan tsarin gurbin hadda, wanda ya kunshi danganta bayanin da kake son ka koya da bayanin da kake da shi daman a kwakwalwarka.