ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Bude Kofa Ta Shaida Niyyar Sin Ta Ingiza Dunkulewar Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

Al’ummar yankin Latin Amurka sun shiga wannan mako da kafar dama, biyo bayan manufar gwajin da kasar Sin ta fara aiwatarwa a ranar Lahadin da ta gabata, na ba ’yan kasashen Brazil da Argentina da Chile da Peru da ma Uruguay, damar shigowa kasar ba tare da biza ba har na tsawon kwanaki 30, domin gudanar da harkokin da suka shafi kasuwanci da ziyara da bude ido da yada zango ko kuma harkokin da suka shafi al’adu. 

Babu makawa, duk abun da kasar Sin ta furta, to da gaske take. Kuma duk burin da ta sanya a gaba, za ta dage wajen kai wa ga cimma masa. Cikin rahoton aikin gwamnati da aka fitar yayin manyan taruka biyu da aka yi a watan Maris na bana, gwamnatin kasar Sin ta nanata niyyarta ta fadada bude kofa, tana cewa ba tare da la’akari da duk wani sauyi da duniya za ta tsinci kanta ciki ba, Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje. Wannan ya nuna muradin kasar Sin na ganin kasashen duniya sun samu ci gaba na bai daya da inganta huldar tsakanin sassan duniya da ma goyon bayanta ga dunkulewar tattalin arzikin duniya.

  • Masani Kwadifwa: Kasar Sin Ce Mai Kare Tabbatuwar Adalci A Duniya
  • Darajar Hajojin Da Aka Yi Jigilarsu a Kasuwar Sin Daga Watan Janairu Zuwa Na Afrilu Ta Karu Da 5.6% 

A yanayin da aka shiga a duniya, babu wata kasa ko al’umma da za ta kebe kanta ita kadai ko rufe kofarta, sannan ta yi tsammanin samun ci gaba ko fifiko kan sauran kasashe. Kulle kofa da wasu kasashe ke son yi, ba zai kai ga muradin da ake son cimmawa na tabbatar da zaman lafiya da habakar tattalin arzikin duniya ba. Mun gani a baya-bayan nan, yadda harkokin cinikayya da tsarin samar da kayayyaki suka hargitse biyo bayan ra’ayin kariya da neman iko.

ADVERTISEMENT

Galibin matsalolin da ake samu tsakanin kasa da kasa da al’ummomin duniya, ya samo asali ne daga rashin fahimta ko yaduwar karairayi, amma cudanyar kasa da kasa da al’ummominsu ta hanyar bude kofa da maraba da juna, zai kara ba da damar fahimta da warware gaskiya da karya, ta yadda za a kai ga inganta fahimtar juna. Wannan na nuna cewa, bude kofa bai tsaya ga amfanawa bangaren tattalin arziki da cinikayya ba kadai, ya kai ga daukaka zaman lafiya da kyautata zamantakewa da samun ci gaba da samar da aikin yi da wayewar kai da kirkire-kirkire da sauransu.

Zuwa yanzu, matakin Sin game da bizar a bana, bai tsaya kan kasashen Latin Amurka ba, su ma ’yan kasashen Saudiyya da Oman da Kuwait da Bahrain, za su more wannan dama daga ranar 9 ga watan nan, har zuwa 8 ga watan Yunin 2026. Haka kuma, an fadada tsarin yada zango na tsawon sa’o’i 240 ga matafiya daga kasashe 54 ba tare da biza ba.

LABARAI MASU NASABA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Irin manufar bude kofa da gyare-gyare ta kasar Sin duniya da jama’arta suka fi bukata, domin ita ce za ta bada damar samun dunkulewar duniya da ci gabanta kamar yadda ake fata, har ma da kai wa gina duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkannin dan adam. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
Next Post
Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Agaji A Borno

Zulum Ya Yaba Wa Sojoji Kan Kashe Babban Kwamandan ISWAP Abu Fatima

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.