Shekaru 19 bayan katse hulda, kasar Nauru ta sake daga tutar kasar Sin a kasar a jiya Litinin, lamarin da ya shaida dawowar huldar dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Hakika wannan na nuna cewa, kasashen duniya sun yi na’am da cewa, Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin daya ce a duniya, kuma ita ce mai wakiltar dukkan yankunanta. Haka kuma ya tabbatar da cewa, duniya baki daya na bukatar kasar Sin, musamman ma kasashe masu tasowa domin ta ba su murya, ta zama musu wata madogara, kuma abokiyar kwarai da za a iya dogaro kanta, haka kuma ta zama abun koyi da misali na neman hanyoyin ci gaba da ya dace da su.
- Dennis Francis: Kasar Sin Ce Mai Jagorantar Kiyaye Ka’idodjin Bangarori Daban Daban Da Inganta Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
- CMG Ya Kaddamar Da Biki Kafin Liyafar Bikin Bazara A New York
Misali, daga dawo da hulda tsakanin Sin da Nauru, kasar Sin ta fara aikin inganta tashar ruwa mafi girma a kasar. Tabbas hadin gwiwa da kasar Sin alheri ne, domin an ce Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta. Na kuma tabbata wannan sabuwar dangantaka, za ta budewa Nauru kofofin samun ci gaba da ba ta samu a shekaru 19 da suka gabata. Kasar Sin ta yi an gani, domin dukkan kasashen dake hadin gwiwa da ita, suna ganin alfanun hakan, ta yadda ta kan taimaka musu a lokacin bukata da kuma ingiza ci gaba a kasashen.
Baya ga haka, manufar kasar Sin daya tak, matsaya ce da MDD da kasashen duniya suka amince da ita. Don haka, kamata ya yi a rika girmama wannan manufa kamar sauran dokokin kasa da kasa. Kasar Sin ta sha nanata cewa, Taiwan wani yanki nata ne da ba zai iya ballewa ba, duk da masu rura wutar rikici da neman ballewar yankin, Sin za ta cimma burinta na dunkulewar baki dayan kasarta cikin lumana.
Yadda a hankali kasashe suke gane cewa amincewa da manufar Sin daya tak, ya nuna cewa, kai na kara wayewa kuma suna kara gane rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin duniya da suka shafi muhimman batutuwa kamar tattalin arziki da ci gaba da wadata da tsaro da zaman lafiya da sauransu.