ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Sin Ta Baiwa Kasashe Damar Shigowa Kasarta Ba Tare Da Biza Ba Za Ta Bunkasa Mu’amala Tsakanin Jama’a Da Jama’a

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a ranar 24 ga watan Nuwamba cewa, kasar Sin ta yanke shawarar gwada tsarin baiwa karin kasashe damar shiga kasar ba tare da biza ba, wanda ya shafi tsawaita zaman matafiya masu rike da fasfo na kasa da kasa daga kasashe shida, wato Faransa, Jamus, Italiya, Netherlands, Spain, da Malaysia.

Wato abin nufi shi ne, daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023, zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, ’yan wadannan kasashe guda shida da ke shiga kasar Sin don kasuwanci, da yawon bude ido, da ziyartar ’yan uwa da abokan arziki, ko kuma yada zango na tsawon kwanaki 15, ba za su bukaci biza ba. Duk da cewa shirin na gwaji ne kamar yadda aka tsara. Amma idan shirin ya yi nasara kuma bai haifar da cikas ko wasu batutuwan da za su shafi zamantakewar al’umma ba, to ba mamaki shirin zai ci gaba da zama na dindindin.

  • Za Mu Samar Da Wutar Lantarki MW60 Ko Sola MW50 A Kowace Jiha -Gwamnonin Arewa Maso-Gabas
  • Tanzaniya Ta Yaba Wa Kasar Sin Game Da Hadin Gwiwa A Fannin Ilimin Fasaha Da Na Sana’a

Shirin yana da mahimmanci ta hanyoyi da yawa, yawancin tsarin shiga kasa ba tare da biza ba, ana gudanar da shi ne bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, wanda ke nufin kasar mai shigowa ita ma dole ta tanadi kwatankwacin tsarin ga Sinawa.

ADVERTISEMENT

Hikimar dake cikin yadda kafofin watsa labaru suka fassara wannan matakin na Beijing shi ne, tsarin na da manufar jawo hankalin masu yawon bude ido daga wadannan kasashe. Saboda shekaru uku da aka yi ana fama da cutar ta COVID-19 ya yi tasiri sosai ga masana’antar yawon shakatawa ta duniya, saboda haka wannan manufa ce da za ta dora wannan fannin tattalin arziki bisa kyakkyawar turba.

A farkon watan Nuwamba, kasar Sin ta fadada manufofinta na yada zango a kasar ba tare da biza ba zuwa ga kasashe 54. Manyan jami’an gwamnatocin kasashen waje da suka hada da ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna, da jakadiyar Jamus a kasar Sin Patricia Flor, sun yaba da wannan yunkurin inda suka yi tsokaci cewa, “Wannan yunkuri ne mai kyau kuma zai saukaka balaguro zuwa kasar Sin ga ’yan kasashen waje da dama da ba a taba ganin irinsa ba.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

A ganina, wannan sabon matakin ya wuce kawai don jawo hankalin masu yawon bude ido. Mataki ne dake nuni da yadda kasar Sin ta ci gaba da bude kofa ga kasashen duniya, da ci gaba da cudanya da sauran kasashen duniya, da ci gaba da yin mu’amala tsakanin jama’a da duniya. Fatana a nan shi ne a nan gaba, kasar Sin za ta shigar da karin kasashe masu tasowa cikin wannan tsarin musamman ma kasashen nahiyar Afirka. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Sabon Nau’in Ciniki Dake Haifar Da Ci Gaba Ga Afrika Da Sin

Sabon Nau’in Ciniki Dake Haifar Da Ci Gaba Ga Afrika Da Sin

LABARAI MASU NASABA

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.