A yayin da duniya ke samun ci gaba cikin sauri, kasashe suna ta kara kaimi wajen kiyaye muradun kasashensu a cikin sauye-sauyen yanayi na duniya. Ga Nijeriya, kasa wacce take da dimbin tarihin jagoranci a nahiyar Afirka, samun daidaito ga wadannan sabbin sauye-sauyen ba kawai zabi ba ne, a’a abu ne da ya zama wajibi kuma mai muhimmanci.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta nemi sake fasalin tsarin manufofin huldar Nijeriya da kasashen waje a karkashin inuwar “Sabuwar Fata” – wani shiri mai karfi, mai kuma cike da buri.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
- Tsaftace Soshiyyal Midiya: Kawu Ya Shirya Taron Kawo Gyara A Kano
Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, wanda ya bayyana wadannan manufofin a ranar 11 ga watan Disamba, 2023, ya bayyana su da cewa an kafa su ne a kan ginshikan manufofin “4D” (Democracy, Debelopment, Demography and Diaspora) na Harkokin Hulda da Waje na Nijeriya: wato Dimokuradiyya, Ci gaba, alkaluma, da kuma Kasashen waje. Wannan hangen nesa yana da nufin sake mayar da Nijeriya kan hannya domin fuskantar kalubale na yau da kullum da kuma tabbatar da cewa kasar ta ci gajiyar ayyukan duniya.
Tun lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, manufofinta na ketare sun kasance ba su canza ba. A kodayaushe Afirka ta kasance jigon manufofin Nijeriya na ketare, wanda kasar ke bin su da karfi – tun kama daga goyon bayan ‘yantar da nahiyar daga turawan mulkin mallaka zuwa tunkarar kalubalen zamani. Nijeriya ta taka rawar gani a fafutikar kwato ‘yancin kai a fadin Afirka, ciki har da taimakawa Afirka ta Kudu wajen yaki da wariyar launin fata.
Bugu da kari kuma, gudummawar da Nijeriya ke bayarwa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya ba za su misalta tu ba, wanda hakan ke jaddada aniyarta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manufofinta na kasashen waje a al’adance suna nufin ingantawa da kuma kare muradun Nijeriya tare da tallafa wa hadin kan Afirka.
Gabatar da ajandar “4D”, a sakamakon haka, yana wakiltar sauyin da aka samu a lokacin da ya dace, wanda hakan zai bude damar karfafa hadin gwiwar da kasashen duniya, tabbatar da zaman lafiya na duniya, da kuma bunkasa matsayin Nijeriya a idon duniya. Sai dai, nasarar wadannan manufofin ya ta’allaka ne a kan aiwatarwar su mai inganci.
Ya kamata a lura da cewa Nijeriya ta tsunduma cikin harkokin diflomasiyya da dama a bara, ciki har da kulla wasu muhimman yarjejeniyoyi da Jamhuriyar kasar Sin. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci Abuja, domin jaddada alkawuran da aka dauka a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2024, inda aka rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi guda 10. Hakazalika, firaministan Indiya Narendra Modi ya ziyarci Nijeriya, inda ya bayyana aniyar kasarsa na zuba hannun jari a wasu muhimman sassa kamar a bangaren noma, samar da abinci, sadarwa, fasaha da bayanai, da kuma tsaro.
Shugaba Tinubu ya kuma gudanar da rangadin diflomasiyya, inda ya halarci taron G20 a Brazil da kuma kai ziyara a Faransa da Afirka ta Kudu da dai sauransu. Wadannan alkawurra an yi su ne da nufin karfafa martabar Nijeriya a idon duniya da kuma samar da fa’idodi na gaske ga kasar.
Duk da yake wadannan tafiye-tafiye na diflomasiyya abin yabawa ne, amma kuma dole ne su kasance su samar wa da kasar jari mai ma’ana da fa’ida ga ‘yan Nijeriya.
Sai dai a halin yanzu, hakan ya yi nisa daga zahirin abin da yake faruwa. Dole ne gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu muhimmanci domin tabbatar da cewa manufofin kasashen waje na Nijeriya sun fifita muradun kasa tare da kare ‘yan kasarta a kasashen waje. Wannan shi ne ainihin manufar “4D”.
Za a iya danganta raguwar tasirin Nijeriya a fagen duniya da tabarbarewar tattalin arzikin da aka shafe tsawon shekaru ana yi, wanda ya tilastawa ‘yan kasar da dama neman ingantacciyar damammaki a kasashen waje, galibi a cikin yanayi mai wahala da wulakanci. Idan ana son a sauya wannan hali, dole ne gwamnatin Tinubu ta gaggauta farfado da tattalin arzikin kasar domin fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci.
Ana iya cimma wannan ta hanyar jawo hankalin masu zuba hannun jari daga kasashe irin su Indiya, Sin, Afirka ta Kudu, da Faransa, musamman a fannoni kamar hakar ma’adinai, aikin gona, da ICT, wadanda ke da fa’ida masu yawan gaske. Har ila yau, dole ne Nijeriya ta mayar da hankali wajen bunkasa harkokin kasuwanci na yanki, kamar samar da kasuwar samun kayayyakin amfanin gona da za su hada masu samarwa da masu shigo da kayayyaki, ta yadda za a rage dogaro da kuma fadada kasuwancin kayayyakin Nijeriya.
Domin manufofin Nijeriya na kasashen waje su yi tasiri, dole ne ta fara magance bukatun ‘yan kasarta. Gwamnatocin da suka gada sun yi ta fafutika wajen yin amfani da damar hadin gwiwar kasa da kasa domin samar da ayyukan yi, da jawo jari, da kawar da talauci. Alkaluman sun yi muni: a tsakanin 2023 zuwa 2024, kashi 63% na ‘yan Nijeriya – kimanin mutane miliyan 133.3 – suna rayuwa cikin kangin talauci, a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS). Rashin aikin yi na matasa ya kasance wani muhimmin batu, a yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 34.6% a karshen shekarar 2024, inda hauhawar farashin kayayyakin abinci ma ya fi kamari.
Rahoton Tattalin Arziki na Afirka (ERA 2023) ya jaddada gaggawar magance kalubalen tattalin arzikin Nijeriya. Ya gano manyan gibi guda uku – kwarewa, abubuwan more rayuwa, da kuma ingancin cibiyoyin (gudanarwa) – wadanda dole ne a gyara su domin gina tubuli mai karfi domin ci gaba.
Mun yi imani wannan ita ce hanya madaidaiciya. Dole ne gwamnatin Tinubu ta fito da tsare-tsare masu kyau na ci gaban kasa, samar da shugabanci nagari, da aiwatar da gyare-gyaren tsari a dukkan bangarori masu muhimmanci.
A yayin da Nijeriya ke fuskantar tabarbarewar tattalin arziki da kuma yanayi na cire fata a tsakanin ‘yan kasar, dole ne gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye tare da rungumar tsarin hulda da kasashen waje na Ambasada Yusuf Tuggar. Manufofin kasashen waje da zai jawo zuba hannun jari, samar da ayyukan yi, da magance tushen talauci, tabbas wadannan a karshe za su samar da nasara. Da duk wani abu da ka iya rage barazana ga barin Nijeriya ta makale a tsaka mai wuya a tsakanin yiwuwarsa da tabarbarewar ta.