Akwai manyan batutuwa guda 7 da za su turnike zauren majalisa bayan dawowa daga dogon hutu na tsawan watanni takwas.
A lokacin da ‘yan majalisar suke hutu, ‘yan Nijeriya a ko’ina a fadin kasar nan sun fuskanci tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashi kayayyaki da ke ci gaba da jefa ‘yan kasan ciki mawuyacin hali saboda manufofin gwamnati.
- DSS Sun Cafke Dan Jarida A Filin Jirgin Sama Akan Hanyarsa Ta Zuwa Umrah Daga Kano
- Babu Wata Yarjejeniya Tsakaninmu Da Gwamnatin Tarayya Kan Dakatar Da Yajin Aiki – NLC
Manyan batutuwan 7 da za su turnike zauren majalisa bayan dawowa hutu sun hada da:
Tabbatar Da Gwamnan CBN
A makon da ya gabata ne, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Yemi Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) tare da mataimakansa guda hudu, sannan suka fara aiki nan take a matsayin rikon kwarya.
Nadin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafan sadarwa, inda ‘yan Nijeriya suka shiga rudani kan makoman Godwin Emefiele. Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan nadin Mista Cardoso a daidai lokacin da ake ci gaba da dakatar da Mista Emefiele.
Sai dai kuma a cikin wata sanarwar da daraktar yada labarai na CBN, Isa AbdulMumin ya fitar a makon da ya gabata, ya bayyana cewa tuni dai Mista Emefiele ya yi murabus.
A wannan makon ne ‘yan majalisar dattawa suka gudanar da aikin tantancewa shi a kan wannan mukami. Sai dai kuma Mista Cardoso yana fuskantar adawa daga wasu sanatoci wadanda suke nuna damuwa kan abin da suka siffanta da “bunkasa tattalin arzikin bangaren Yarbawa”.
Matakin da shugaban kasa ya dauka na nada Cardoso a matsayin wanda zai maye gurbin Emefiele da kuma mukaddashin hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS), Zacch Adedeji bai faranta wa mafi yawanci sanatocin arewa rai ba.
Tabbatar Da Sabbin Ministoci
Wani tabbacin kuma shi ne na sabbin ministoci da Shugaba Tinubu ya nada. Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Tinubu ya nada Jamaila Ibrahim da Ayodele Olawande a matsayin ministocin matasa.
Ana tsammanin cewa a wannan makon ne sanatoci za su tabbatar da nadinsu.
Har ila yau, akwai batun Nasir el-Rufai da sauran wadanda majalisa ta tantance. Majalisar dattawa ba ta wanke tsohon gwamnan Jihar Kaduna ba sakamakon rahotannin tsaro. Sai dai kuma har yanzu Shugaban Tinubu bai nada wanda zai maye gurbinsa ba, wanda ya nuna cewa ya kebe wa Jihar Kaduna ma’aikatan muhalli.
Yayin da kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewa el-Rufai ya fice daga kasar, amma duk da haka shugaban kasa bai zabi wanda zai maye gurbinsa ba, kallo ya koma kan majalisar dattawa dangane da matsayin el-Rufai.
Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashi
A makon da ta gabata, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC), Festus Osifo ya sanar da cewa kungiyar tana sa ran shugaban kasa zai bayyana sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dakile radadin cire tallafin man fetur.
Tsarin mafi karancin albashin yana cikin kebattancen jerin dokokin majalisa da ke cikin kundin tsarin mulki. Domin haka, majalisa na da ikon yin doka kan sabon tsarin mafi karancin albashi. Ana sa ran za ta amshi kudurin sabon tsarin mafi karancin albashi daga bangaren zartarwa.
Kasafin Kudi
A daidai lokacin da majalisa ta dawo hutu, ‘yan Nijeriya za su sami damar ganin alkiblar kasafin kudin Shugaba Tinubu na farko da zai gabatar a gaban zauren majalisun kasa guda biyu.
Idan za a iya tunawa dai shugaban kasa ya yi alkawarin sake duba manufofin kasafin kudin kasar nan idan har aka zabe shi, kasafin kudin zai bayar da damar sanin abin da ya fi bai wa fifiko.
Abin da aka saba shi ne, majalisar kasa za ta bayar da matsakaicin tsarin kasafin kudi da kuma dubarun kasafin kudin da ke rubuci a takarda kamar yadda dokar kasafin kudin ta tanada, sai dai har yanzu takardun kasafin kudin guda biyu ba su kai ga isa zauren majalisa ba.
Haka kuma majalisar dokokin kasa na iya ci gaba da gudanar da tsarin kasafi daga Janairu zuwa Disamba domin tabbatar da amincewa da kasafin kudin 2024 kafin a tafi hutun watan Disamba.
Batun Harkokin Tsaro
A kwanakin baya ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai mata na jami’ar tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, sai dai kuma sojoji sun ceto wasu daliban, yayin da sauran ake ci gaba da garkuwa da su.
Baya ga na Jihar Zamfara, ‘yan Nijeriya a fadin kasar nan suna ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro da suka hada da ‘yan bindiga a yankin arewa da kuma masu tayar da kayar baya a yankin kudu maso gabas.
Yayin da ‘yan majalisa suka dawo hutu, ‘yan Nijeriya suna tsammanin ganin matakin da ‘yan majalisar za su dauka kan lamarin.
Binciken Musabbabin Mutuwar Mohbad
A makon jiya, dan majalisa daga Jihar Delta, Ned Nwoko ya sanar da cewa zai gabatar da kudurin doka domin wajabta gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar Mawaki, Mohbad.
Sanata Nwoko ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ke ce-ce-ku-ce game da musabbabin mutuwar mawaki, Mohbad.
Gabatar da irin wannan kudirin doka na iya haifar da muhawara ga ‘yan majalisan game da musabbabin mutuwar mawaki Afrobeat. Idan za a iya tuwa, Sanata Elisha Abbo ya ziyarci mahifiyar mawakin.
Yayin da ‘yan majalsar suka dawo hutu, akwai yuwuwar a tafka muhawara game da musabbabin mutuwar mawakin.
Batun Rade-radin Shirin Tsige Akpabio
A lokacin da ‘yan majalisa suke hutu, an yi ta rade-radin cewa wasu sanatoci na shirin tsige shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, musamman ‘yan majalisa daga yankin arewacin Nijeriya.
An bayyana cewa har yanzu akwai batun a tsakanin wasu tsirarun ‘yan majalisar, yayin da wasu ‘yan majalisar kotunci suka yi wa tsohon gwamnan Akwa Ibom.
Lokacin da ‘yan majalisa suka dawo hutu, lamarin zai bayyana a fili kan asalin batun gaskiyar tsige shugaban majalisar dattawan.