Ko shakka babu, fannin kiwon Zuma a Nijeriya na da matukar tsawon tarihi, musamman wajen hawa da sauka da kuma fannin tattalin arziki ga masu wannan sana’a a fadin kasar nan.
Dabarun Kiwon Zuma A Gargajiyance:
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
Kiwon Zuma ba sabon abu ba ne a tsakanin al’ummar Afirka, domin kuwa an shafe shekara da shekaru ana yi, musamman a yankunan Sahel.
Har ila yau, kasancewar ganin ana samun karancin Katako da Timba a yankunan na Sahel, ya sa masu yin wannan kiwo fara amfani da Tukwane da kuma Ciyawa, don yin kiwon zuma wanda wasu ke ganin wadannan a matsayin kayan gargajiya, wadanda kuma suka fi dacewa da wannan kiwo a Nijeriya.
Wasu daga cikin masu wannan kiwo na zuma, sun fi son gina gidan zumar a kasa, domin kuwa a nasu ganin da kuma ilimin; wadanan gidaje sun fi jima, don kuwa suna kai wa har zuwa karshen shekara ba tare da an sauya musu wani gidan daban ba.
Wannan dabarar kiwon zuma a gargajiyance, na daya daga cikin dabarun da ake amfani da ita a Nijeriya. Nau’i na farko da ake amfani da shi wajen wannan kiwo na zuma shi ne, amfani da Tukunya; sai kuma nau’i na biyu da ake ginawa a kan Tukunya. Dukkannin wadanannan nau’ika biyu, ana dora su ne a tsakanin Gwafar bishiya.
Amfani Da Tukunyar Laka A Matsayin Gidan Kiwon Zuma:
Wannan hanya kusan ta fi sauki, sannan kuma ita ce hanya mafi sauki tare da juriya wajen kiwon wannan zuma a gargajiyance.
Dabarun Kiwon Zuma A Zamanance:
Mafi akasarin wannan dabara ta kiwon zuma a zamanance, Lorenzo Lorraine Langstroth ne ya samar da ita.
Har ila yau, wannan hanya na da matukar sauki; domin kuwa akasari bayan zuma ta kammala gina gidanta, sukan tashi su kuma shiga wani dakin zuman daban.
Haka zalika, mafi yawan sauran gidajen zuma na zamani da ake gani a yau, dabaru ne da aka samu daga wurin Langstroth; wanda kuma ake yi masa lakabi da jagoran ginin gidan kiwon zuma na zamani.
Wannan hanya ta zamani, na daya daga cikin wadda ake amfani da ita a Nijeriya, wajen kiwon zuma.
Kazalika, a wannanbangare; zumar ce da kanta ke gina dakin nata na kwana, amma inda matsalar take kadar shi ne na rashin samar wa da dakin wata kariya, domin kuwa zai iya karyewa a cikin sauki.
Sai dai, masu sarrafa irin wannan daki na kiwon zuma; na bukatar amfani da injinan da ke aiki da wutar lantarki, wanda hakan zai bai wa zumar damar zuba tukarta a cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
Har ila yau, akwai kuma irin wannan dabarar; wadda Farfesa G.F. Townsend na jami’ar Guelph da ke Kasar Kanada ya kirkiro da ita.
Mafi akasarin lokuta, an fi amfani da wannan dabara; wajen zuba zuma mai fada wadda aka fi samu a yankunan Afirka.
An kuma fi bai wa wanda zai fara wannan kiwo na zuma shawarar yin amfani da wannan dabara, domin kusan ta fi sauki.