Manyan jami’an JKS sun mika rahoton ayyukansu ga kwamitin tsakiya na jam’iyyar da ma sakatare janar na kwamitin kuma shugaban kasa Xi Jinping.
Jami’an sun hada da mambobin ofishin siyasa da sakatariyar kwamitin kolin JKS da mambobin manyan rukunonin kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’a da na majalisar gudanarwa ta kasa da na kwamitin kasa na majalisar ba da shwarwari kan harkokion siyasa da sakatarorin manyan rukunoni na kotun koli da hukumar koli ta bin bahasi ta jama’ar kasar.
Bayan nazartar rahotannin, shugaba Xi ya bukaci jami’an mayar da hankali kan inganta zamanantar da kasar Sin da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da karfafa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a harkokin siyasa da yin iyakar kokari cikin hadin kai wajen gina kasa mai karfi tare da inganta farfadowarta. (Fa’iza Mustapha)