Yau Laraba 19 ga wata, mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma daraktan ofishin lura da harkokin kasashen waje na kwamitin kolin Wang Yi, ya gana da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Henry Kissinger a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar ta su Wang ya bayyana cewa, manufofin kasar Sin ga Amurka na da alaka da juna, wadanda ke kan ka’idojin girmama juna, da kasancewa cikin yanayi na zaman lafiya, da hadin kai don samun nasara tare, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Wadannan ka’idoji sun kasance hanya mai dacewa, ta raya dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu wato Sin da Amurka. Kaza lika kasar Sin na da karfin kara samun bunkasuwa, hakan kuma na bin yanayin ci gaban tarihi. Kuma ba zai yiwu a yi yunkurin canja hanyar ci gaban Sin ba, haka kuma ba zai yiwu a nemi hana ci gaban Sin ba.
A nasa bangaren, Mr. Kissinger ya furta cewa, Amurka da Sin kasashe ne da ke da babban tasiri a duniya. Batun tabbatar da raya dangantaka a tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata, na da nasaba da cimma nasarar zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da alfanun al’ummomin duniya baki daya.
Kissinger ya kara da cewa, komin wahalhalun da suke fuskanta, ya kamata bangarorin biyu su nuna wa juna daidaito, da kiyaye tuntubar juna. Ya ce ba za a amince da a nuna wa juna wariya ba. Kuma kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, alkawari ne da kasar Amurka ta yi a cikin Sanarwar Shanghai da aka fitar a shekarar 1972. Kuma an yi imanin cewa ba za a canza da karya wannan alkawari ba.
Ban da haka kuma, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan tsaron kasar janar Li Shangfu ya gana da Kissinger yau a Beijing.
Li ya ce, a wannan duniya mai cike da rudani da sauye-sauye, jama’ar dukkan kasashe suna fatan Sin da Amurka za su sauke nauyin da ke wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe, tare da kiyaye wadata da kwanciyar hankali a duniya baki daya.
Li ya bayyana fatan cewa, Amurka za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da ra’ayin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sojojinsu.
Kissinger, a nasa bangaren ya ce a duniya ta yau, kalubale da damammaki suna cudanya, don haka ya kamata Amurka da Sin su kawar da rashin fahimtar juna, su zauna tare cikin lumana, da kuma kaucewa fada.
Ya bayyana fatan bangarorin biyu za su yi amfani da hikima, da yin duk wani kokari na samar da sakamako mai kyau don raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Kande Gao &Yahaya Babs)