Kwamitin hadaka na manyan makaratun guda biyar da ke jihar Bauchi (JAC), sun ayyana tafiya yajin aikin jan kunne na tsawon kwanaki 14 da zai fara aiki daga ranar Laraba 19 ga watan Yuli zuwa ranar Lahadi 30 ga watan Yulin 2022 domin jawo hankalin Gwamnatin jihar Bauchi da ta share musu hawayensu.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a wani taron da suka kira, Shugaban JAC, Abdulkadir Mohammed, ya ce bukatun da suke da su, sun kunshi a gaggauta biyan albashin dukkanin mambobin kungiyar ke bi ba tare da bata wani lokaci ba.
Wakilinmu ya nakalto cewa hadakar makaratun sun hada da Kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere da Kwalejin ilimi, koyar da ilimin shari’a da sashin ilimin komai da ruwanka ta A.D Rufa’i da ke Misau da Kwalejin ilimi ta Aminu Saleh da ke garin Azare da Kwalejin Ilimi da Koyon aikin gona ta jihar Bauchi da kuma babbar Kwalejin Kimiyya, fasaha da kere-kere mallakin gwamantin jihar Bauchi, ATAP.
Kazalika, kwamitin ya yi kira da a gaggauta dawo da aiwatar da tsarin karin girma na shekara-shekara ga wadanda suka dace da aka dakatar da yi ba tare da an bayyana a hukumance dalilin dakatarwar ba tun lokacin da gwamnati mai ci ta hau kan mulki.
Shugaban kungiyar ya ce kwamitin nasu ya nuna adawarsa kan shigar da ma’aikata tsarin taimakekeniya ta fansho duk kuwa da cewa hatta ma’aikatan Gwamnatin tarayya ma na kaurace wa tsarin domin wahalar da ke janyo wa ma’aikatan.
A cewarsa, su na kuma da bukatar a dauki dukkanin matakan da suka dace wajen samar wa mambobin kungiyar rayuwa mai inganci da kuma tsaron hakkokinsu a kowani lokaci domin samun dama da sararin gudanar da aiki ba tare da wani fargaba ko dar-dar ba.
Abdulkadir Mohammed ya ce sun kuma yi adawa da cire wani kaso daga cikin albashin ma’aikatan da sunan shirin tallafin gidauniyar kiwon lafiya da ake kira BASHMA.
Mohammed ya ce bisa wadannan dalilai da sauran hakkokinsu da suke nema ne ya sanya suka zauna suka cimma matsayar tafiya yajin aikin gargadi, kodayake kafin wannan ya ce sun bai wa gwamantin wa’adi da jawo hankalinta tun da jimawa amma matsalolin nasu sai karuwa suke yi. Don haka ne suka ga dacewar tafiya yajin aikin.
Ya cigaba da cewa domin neman adalci dai, sun tuntubi hukumomin da abun ya shafa kan matsalolin nasu domin ganin an yi shawo kan kalubalen da suka hada da Akanta Janar na jihar, da kwamishinan ilimi, da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, duk da tilin wasikun da suka aike musu.
“Mun rubuta wasika muka aike wa mai girma gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir a tunanin mu duk abun da suke faruwa bai ma san da su ba. Nan ma dai ba mu samu sauyi ko canji daga matsalolinmu ba.”