Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Imo da kuma Bayelsa.
Za a gudanar da zabukan jihohin ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
A tsawon watanni bakwai da suka wuce, ‘yan takarar gwamna a jihar Kogi, na ta gudanar da yakin neman zabe a kokarin su na ganin sun kai ga nasara.
Yanzu haka akwai ‘yan takara 18 da ke takarar gwamnan a jihar ta Kogi.
‘Yan takarar za su fafata ne domin ganin wanda zai maye gurbin gwamna Yahaya Bello mai barin gado, wanda ke kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu.
Jam’iyyar APC mai mulkin jihar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta rike kujerar gwamnan yayin da jam’iyyun adawa kuma ke kokarin ganin sun kwace mulki daga hannun APC da ke kan mulki tsawon shekaru takwas.
Cikin jam’iyyu 18 da INEC ta tantance domin shiga zaben gwamna a jihar Kogi ya zuwa ranar 9 ga watan Nuwamban, 2023, ana ganin cewa shida ne kawai ke a kan gaba gabanin zaben na ranar Asabar.
Masana harkokin siyasa a jihar na ganin cewa fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin jam’iyyu uku; APC, PDP, da kuma SDP.
Masanan sun kara da cewa manyan ‘yan takarar uku da ke sahun gaba a zaben sun fito ne daga kabilu daban-daban, kamar Ebira, Igala, da kuma Okun, kuma hakan zai iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaben.
Sun ce yayin da jam’iyyar APC za ta iya samun yawan kuri’u daga tsakiyar jihar, SDP kuma za ta iya bayar da mamaki a gabashin jihar, inda ita kuma PDP mai dimbin magoya baya a yammacin jihar, za su zabi Dino Melaye.
Manyan ‘yan takarar guda uku da za su fafatawa a tsakaninsu su ne:
Sanata Dino Melaye – PDP
Sanata Dino Melaye shi ne mutumin da zai yi wa jam’iyyar PDP takara a zaben gwamnan Kogi a yau Asabar.
An haife shi ne a watan Janairun 1974 kuma dan siyasa ne mai yawan haifar da cece-kuce.
Tsohon Sanatan, ya yi karatun sakandare a Kwalejin Abdulaziz Attah, da ke Okene.
Daga nan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2000 inda ya karanta ilimin Geography.
A shekara ta 2021, ya kammala karatu a Jami’ar Baze, inda ya karanta fannin Shari’a.
Melaye ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa daga 2015-2019.
Zamansa dan takarar jam’iyyar PDP, ya kara iza wutar adawa tsakaninsa da jam’iyyar APC a jihar.
Ana kuma ganin cewa dimbin magoya bayan jam’iyyar PDP na tare da shi, kuma suna shirye domin zaben shi a matsayin gwamnan jihar Kogi.
Ododo Ahmed Usman – APC
Ododo Usman shi ne dan takarar zaben gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC a zaben da za a yi.
Usman-Ododo wanda dan kabilar Ebira ne da ya fito daga garin Okene, ya yi digirinsa na farko a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a Jami’ar Legas.
Kafin samun zama dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya kasance babban mai binciken kudi na kananan hukumomin jihar, tsawon shekara bakwai da rabi, kuma an yi imanin cewa ya taka rawar gani a gwamnatin Yahaya Bello.
Murtala Yakubu Ajaka – SDP
Murtala Yakubu Ajaka ya kasance babban jigo a jam’iyyar APC a jihar Kogi, kafin komawarsa SDP.
Mista Ajaka ya fito ne daga karamar hukumar Igalamela, da ke gabashin jihar Kogi. Mazabar tana da yawan masu kada kuri’a.
Ya koma jam’iyyar SDP ne bayan kasa samun tikiti a APC, inda daga bisani ya samu nasarar zama dan takarar SDP a zaden gwamnan Kogi na 2023.
An yi imanin cewa dan takarar na SDP na iya samun kuri’u masu yawa a gabashin Kogi.