Bisa gayyatar da shugaban kasar Gabon Brice Nguema ya yi, Mu Hong, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, ya halarci bikin rantsuwar kama aiki na shugaba Nguema, a birnin Libreville na Gabon, a ranar Asabar da ta gabata. Kana a jiya Lahadi, shugaba Nguema na Gabon ya gana da mista Mu Hong, duk a Libreville din.
Yayin ganawarsu, Mu Hong ya ce kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Gabon, da daga huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon matsayi. A nasa bangare, shugaba Brice Nguema ya ce kasarsa za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin zurfafa hadin kai tare da kasar Sin a bangarori daban daban. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp