Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai dace duk wani dan Nijeriya da ake daukarsa a matsayin dattijo yake nuna goyon bayansa ga wani dan takarar mai neman shugabancin kasar nan a zaben 2023 ba.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a garin Benin, babban birnin Jihar Edo, lokacin sa ya je kaddamar da yakin neman zabensa a jihar.
- A Matsayinta Na Kasa Mafi Yawan Masu Harbuwa Da Cutar COVID-19 A Duniya, Matakin Amurka, Tamkar “Barawo ke cewa ku tare barawo!”
- Shugaban Kasar Saliyo Ya Jinjinawa Kyakkyawar Dangantakar Kasar Sa Da Sin
Ya ce, “Ina so na shawarci shugabaninmu da su daina zubar da mutuncinsu, domin muna girmama su matuka, idan kace baka ra’ayi na, babu wata matsala”.
“Ina ganin wannan babban kuskure ne, domin wadannan shugabanni ne da nake ganin kimarsu.”
Kwankwaso wanda ya sanar da hakan a yayin da gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya karbi bakuncinsa gidan gwamnatin jihar lokacin da ya je kaddamar da yakin neman zabensa.
“ina so na shaida muku cewa, duk dan takara ko kuma jam’iyyar da suka fito fili suka nuna yin amfani da kabilanci ko addini, ina mai tabbatar muku da cewa, sun riga sun sha kasa tun kafin a fara gudanar da zabe.