A wannan makon ne kutunan sauraron kararrakin zaben gwamnoni suka zartar da hukunci a Jihohin Kano, Bauchi da kuma Zamfara, lamarin da ya janyo martani Sai daban-daban kan hukunce-hukuncen kotun.
A ranar Laraba kotun sauraren kararrakin zabe ta zartar da hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Kotun ta kwace kujerar gwamna daga hannun Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai wannan hukunci ya bar baya da kura tare da barin dubban mutane cikin dar-dari da fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo.
Tun da fari dai lauyoyin NNPP sun yi fatali da hukuncin kotun, inda suka ce za su daukaka kara. Magoya bayan jam’iyyar NNPP na ganin an yi bita da kulli wajen kwace musu ‘yancinsu.
A gefe daya kuma, magoya bayan jam’iyyar APC sun shiga murna da shewa tare da fitowa kan wasu tituna na jihar don nuna farin cikinsu kan nasarar da suka samu a kotu.
Sai dai kasuwanni irin su Sabon Gari, Kwari, Wambai, Farm centre da sauransu sun rufe shaguna saboda gudun tashin rikici.
Tuni dai kafafen sada zumunta suka dauki dumi, idan magoya bayan duka manyan jam’iyyun adawa suka shiga bayyana ra’ayoyi mabanbanta.
Tun a ranar Talata ne aka girke daruruwan jami’an tsaro a manyan titunan kwaryar Kano, domin shirin ko ta kwana a yayin zartar da hukuncin.
Da safiyar ranar Laraba ne jagororin kowace jam’iyya suka isa harabar kotun don jin hukuncin da kotun za ta zartar karkashin jagorancin alkali, Oluyemi Akintan-Osadebay.
Sai dai daga bisani aka bayyana cewar za a zartar da hukuncin ne ta Intanet ta hanyar amfani da manhajar ‘Zoom’. A gefe guda kuwa, jami’an tsaro na ci gaba da tabbatar da doka da oda a jihar.
Haka zalika, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Bauchi a ranar Laraba ta tabbatar da nasarar Bala Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a 2023 da ya gudana, inda ta kori karar da dan takarar jam’iyyar APC Sadikue Abubakar ya shigar da ke kalubalantar nasarar Bala. Sai dai kotun ta ce karar bai da madogara don haka ta kori korafin.
Gwamnna Bala ya misalta nasarar da ya samu daga Allah ne, don haka ya nuna matukar godiyarsa a bisa sake zabinsa da al’ummar jihar suka yi a karo na biyu.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan tabbatar da nasarar, Bala Muhammad ya ce dimukuradiyya ce ta yi halinta, kuma hakan zai kara masa himma da azama wajen ganin ya ci gaba da yin kokarinsa domin sabunta Jihar Bauchi.
Ya nemi hadin guiwar masu ruwa da tsaki ciki har da abokan hamayyarsa da su zo a hada karfi da karfe domin ciyar da Jihar Bauchi gaba.
Da yake nuna farin cikinsa bisa wannan nasarar, Kakakin Majalisar dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Y Sulaiman ya nuna gayar farin cikinsa bisa nasarar da Bala Muhammad ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben.
A wata sanarwa da mai Magana da yawunsa, Abdul Ahmed Burra ya fitar, Abubakar ya nemi al’ummar jihar da su ci gaba da mara wa gwamnati da majalisar dokokin jihar baya domin sauke nauyin da ke gabansu.
Daya daga cikin kwamitin yada labarai na dan takarar APC da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa suna kan nazarta hukuncin domin daukan mataki na gaba.
“Muna kan nazartar hukuncin kuma in sha Allah za a dauki matakin da ya dace cikin gaggawa,” ya shaida.
A bangare guda kuma, kotun sauraran kara ta zabe da ke zamanta a Sakkwato ta tabbatar da nasarar Gwamna Dauda Lawal a matsayin gwamnan Jihar Zamfara.
Al’umma jihar da suka zanta da wakilinmu kan hukuncin, sun bayyana ra’ayoyinsu.
Muhamda Gali ya bayyana cewa gaskiya ce ta yi halinta tun da zabe da aka yi wa gwamna Dauda a bayyane yake babu magudi a zabensa, wanda bai da gwamnatin yaya zai yi magudi.
A cewarsa, jamiyyar APC ta yi hakuri a wannan karon, domin PDP Allah ya tabbatar mata da mulki, kuma wannan ya ishi mutane ishara.
Shi kuwa wani dan jamiyyar APC da ya nemi na sakaya sunansa ya bayyana cewa, “Mu ne muka jawo wa kanmu faduwar zabe, saboda irin kalamun da muke furtawa na cewa tun da ga Matawale ga Shehi dole ne mu ci zabe ba tare da fadin in sha Allah ba, sai gashi Allah ya jarra be mu da rashin cin zaben.
“Allah ya nuna mana ishara. Domin haka, dole jamiyyar APC ta hakura zuwa wani zaben mai zuwa.”