Connect with us

ADABI

Marubuciya Safiyya Jibrin Ta Lashe Gasar Hikayata Ta BBC Hausa 2018

Published

on

Gasar dai mai taken Hikayata wacce gidan rediyon BBC ta ssanya ta gajerun labarai. An fitar da sakamakon gasar ne a safiyar ranar Juma’a da ta gabata 7/9/2018, inda shugaban akalan gasar Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana marubuciya Safiyya Jibrin wacce aka fi sani da Ummu Abdoul a matsayin wacce ta lashe gasar a matakin farko da labarinta mai suna ‘Ya Mace a cikin labarai sama da Dari Uku da suka samu damar shiga gasar.

Labarin ‘Ya Mace a Dunkule
‘Ya Mace, labari ne na wata budurwa mai suna Halima wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 babu wani tsayayye, alhali a bisa al’adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar da ita. Matsin lambar da take fuskanta daga iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri Garba duk da cewa ba a gudanar da wani bincike a kan shi ba.
Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata kunne cewa kada ta kuskura a sake ta don idan ta dawo gida ba shi da halin daukar nauyinta. Sanin hakan ya sa Garba yi wa Halima wulakanci iri-iri, har lamarin ya kai ga duka da zagi.
A karshe dai auren ya mutu; da ta koma gida mahaifinta ya kore ta bayan ya lakada mata duka, sannan ya sha alwashin tsine wa duk wanda ya ba ta masauki a cikin ‘yan uwa.
Wannan ya sa Halima ta yanke shawarar tsayawa da kafafunta ta hanyar kama hayar daki a cikin gari da yin ayyukan hannu don ciyar da kanta. Sai dai ba a jima ba mai gidan ya samu labarin cewa ba ta da miji, ya ba ta notis yana mai cewa bai kamata mace irinta ta zauna a tsakanin mutanen kwarai ba.

Da Me Labarin ‘Ya Mace Ya Yi Zarra?
A cewar alkalan gasar, wannan labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma’aunan da aka yi amfani da su don tantance labarai 25 din da suka duba.
“Labarin ya tabo wata matsala da ke faruwa a wannan zamanin, inda iyaye ke Allah-Allah su aurar da ‘ya’yansu mata. Tun da aka fara labarin ake hawa, ake tashin hankali da jan hankalin
mai karatu”, inji Bilkisu Yusuf Ali, daya daga cikin alkalan.
Jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya kara da cewa, “Matsalar labarin daya ce kawai: tun daga farko har karshe ake hawa, ba sauka. To amma shi ma wata dabara ce ta marubuta”.

Wace Ce Safiyya Jibrin?
Safiyyah Jibril Abubakar malamar makaranatr sakandare ce, kuma daliba mai karatun digiri na biyu, wato Master’s, a fannin Kimiyyar Kasar Noma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Ta yi makarantar firamare a birnin na Zariya, sannan ta yi karatun gaba da firamare a garin Gwandu na Jihar Kebbi.
An fi sanin ta da suna Safiyyah Ummu Abdoul a duniyar marubuta. Labarainta, ‘Ya Mace , shi ne ya zo na daya a gasar Hikayata ta 2018. Safiyya Jibrin ita ce shugabar kungiyar marubuta ta Fikra Writers Association kuma ita ce ta kafa kungiyar. Ta fara rubutu a shekara ta 2013 ta rubuta littattai da dama.

Labarin Da Ya Zo Na Biyu
Labarin da ya zo na biyu shi ne ‘Sunanmu Daya’ na Sakina Lawal. Shi ma labarin wata budurwa ne wadda kyawunta ya rude ta har take ganin duk yadda ta ga dama za ta yi da maza. Da ta samu wani wanda take ganin ya dace ta aura shi kuma yana da mata, sai ta sa ya saki matar, amma bayan ta aure shi sai ta ga ashe dai kallon kitse ta yi wa rogo don haka ta fita.
Daga bisani ta sake samun wani mai matar, amma suna son juna tsakani da Allah. Sai dai kuma bayan ta aure shi sai ta tarar ba wata ba ce matar illa wacce ta sa mijinta na farko ya saka.

Labarin Da Ya Zo Na Uku
Labarin da ya zo na uku shi ne Zaina, wanda Bilkisu Muhammed Abubakar ta rubuta. Shi kuma labari ne na wata mai suna Zaina wacce mijinta ya yi batan dabo bayan tashin bam. Bayan ta shekara shida tana jiran tsammani iyayen mijin suka matsa mata lamba a kan ta sake aure.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: