Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mary Ukaego Odile: ‘Yar-Na-Gada Da Ta Yi Fice A Bangaren Shari’a

by
3 years ago
in FITATTUN MATA
3 min read
Mary Ukaego Odile: ‘Yar-Na-Gada Da Ta Yi Fice A Bangaren Shari’a
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ko-kun-san?

Mary Ukaego Odili, matar tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili ce wacce ta kasance kwararriyar Lauya da ta zama Alkali a kotuna daban-daban tun daga karamin mataki har ga zuwa babban Alkali a kotun koli. Ta taka rawa sosai wajen bayar da gudunmawarta a bangaren shari’a musamman a kotunan da ta yi aiki a manyan kotunan daukaka kara na sashi-sashi a sassa daban-daban na kasar nan. Wani abin burgewa a rayuwarta, ta sha ilimi a bangaren shari’a ne tun daga mahaifinta domin shi kansa Lauya ne.

Wace ce Mary Ukaego?

Labarai Masu Nasaba

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

Mary Ukaego Odili, an haife ta ne a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 1952 a kauyen Amudi Obizi da ke karamar hukumar Ezinihitte-Mbaise a jihar Imo. Mary Ukaego ita ce diya ta biyu a cikin jerin ‘ya’yan Eze Bernard Nzenwa. Babanta Eze shi ma kwararren Lauya ne da ya yi aiki a Ingila a shekarar 1959, kafin daga baya ya zama sakataren hukumar sararin samaniya ta Nijeriya (Nigerian Airways).

Ta halarci makarantun Firamare da dama ga su kamar haka; St Benedict’s Primary School, Obizi Ezinitte, St Michael’s Primary School, Umuahia, St Agnes Primary School, Maryland da kuma Our Lady of Apostles Primary School, da ke Yaba. Daga bisani ta halarci sakandarin Our Lady of Apostles Secondary School da ke Yaba a jihar Legas amma ba ta kammala ba domin kuwa ta je sakandari da daman gaske a sakamakon sauye-sauyen matsuguni da suka yi ta yi.

Biyo bayan barkewar yaki a shekarar 1967, mahaifan Ukaego da ita suka sauya matsuguni zuwa Kudu maso gabashin kasar nan. Ta ci gaba da karatunta a makarantar mata ta Owerri har zuwa lokacin da iyalanta suka kaura zuwa Mbaise. Sannan, ta sake halartar sakandarin ‘yan mata da ke Mbaise. Kana ta nausa makarantar Kueen ta Kwalejin Rosary a Onitsha. A shekarar 1972, ta samu shaidar kammala sakandari. A wannan shekarar ne kuma ta samu iznin shiga jami’a Nijeriya da ke Enugu inda ta karanci bangaren shari’a. a shekarar 1976 ta kammala da shaidar LLB ta samu sakamako mai matukar kyau bangaren shari’a.

Baya ga nan, ta je Nigeriyan Law School domin samun shaidar B.L a shekarar 1977, daga bisani ta yi bautar kasa a Benin City ta jihar Abeokuta.

Aiyukanta:

Madam Ukaego ta fara gudanar da aikinta a bangaren shari’a ne a kotun Majistiri a matsayin Grade III a watan Nuwamban shekarar 1978. Ta auri Odili a shekarar 1979 wanda har suka samu haifar da da suka sa masa suna Adaeze.

Mary Ukaego Odili da ita da iyalanta suka koma zuwa Port Harcour da zama, inda mijinta ya assasa cibiyar kula da lafiya ta Pamo Clinics.

A tsakanin shekarar 1980 da 1988, Mary ta yi aiki a matsayin Babban Alkali a kotun majistiri a matsayin ta I, ta zama shugaban kotun Jubenile, ta zama shugaba, ta zama shugaban hukumar bincike ta Marine a shekarar 1979, ta zama shugaban kwamitin kungiyar tsoffin dalibai a jami’ar Nijeriya, ta zama shugaban kungiyar Lauyoyi mata ta kasa (FIDA), reshen jihar Ribas da kuma zama sakatariya. A shekarar 1992 ne ta zama Alkali a babban kotu ta jihar Ribas har zuwa shekarar 2004. A lokacin da aka zabi mijinta a matsayin gwamnan jihar Ribas, Mary ta zama First Lady na jihar Ribas har zuwa ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2007.

Aikinta a manyan kotuna:

Mary ta kasance wacce ta samu ofis a matsayin mai shari’a daban-daban, ta kasance Alkalin a kotun daukaka kara da ke Abuja daga shekarar 2004 zuwa 2010 da kuma zama a kotun, ta kuma kasance Alkali a kotun daukaka kara da ke reshen Kaduna daga shekarar 2010 zuwa 2011. A ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2011 ne shugaban kasa Jonathan ya zabeta da wasu biyu a matsayin masu shari’a a kotun daukaka kara. Ta kasance wacce ta kula da shiyyar Kudu maso gabas kan hidimar shari’a. daga bisani aka nada ta a matsayin babbar Alkali a kotun daukaka kara ta Nijeriya (JSC) a shekarar 2011.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kofin Duniya Na Mata: Nijeriya Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Next Post

Ya Halatta A Kara Wa Amarya Yawan Kwanaki Saboda ‘Honey Moon’?

Labarai Masu Nasaba

Maryam Ibrahim Shettima

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

by
10 months ago
0

...

Hajiya Kyari Joda

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

by
10 months ago
0

...

Hafsat

Hafsat Ganduje Garkuwa Ga Mijinta A Fannin Shimfida Ayyuka

by
11 months ago
0

...

Farfesar

Adenike Osofisan: Mace Ta Farko Farfesar Kimiyyar Kwamfuta A Nahiyar Afrika

by
1 year ago
0

...

Next Post

Ya Halatta A Kara Wa Amarya Yawan Kwanaki Saboda ‘Honey Moon’?

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: