Adadin wadanda suka mutu sakamakon rushewar babban masallacin Zariya, a yammacin ranar Juma’a a garin Zariya na jihar Kaduna, ya kai 12.
Idan za a tuna cewa lamarin ya afku ne a daidai lokacin da masallata suke gudanar da sallar la’asar da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma’a.
- Tsohon Gwamnan Kwara A Mulkin Soja, Latinwo Ya Kwanta Dama
- Australia Ta Doke Faransa A Bugun Fanareti Inda Ta Kai Zagayen Kusa Da Na Karshe
A halin yanzu, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, da kungiyar Jama’atul Nasir Islam (JNI), sun mika ta’aziyyarsu ga masarautar Zazzau da iyalan wadanda suka rasu.
Gwamna Uba Sani, a cikin ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.
Gwamnan ya gode wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, bisa irin rawar da ya taka wajen hada kan al’ummarsa domin gudanar da aikin ceto, da bayar da taimako ga wadanda suka jikkata da kuma jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.
Gwamnan ya kuma yaba da kokarin wadanda suka fara yin ceto, da ma’aikatan lafiya, da kuma nagari mutanen Zariya wajen ceto wadanda suka tsira.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma kara da cewa tuni tawagar manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Abbas Lawal, ta isa Zariya don tantance halin da ake ciki.
“Gwamnatin jihar za ta kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin,” in ji shi.
“Ina matukar bakin ciki da abin da ya faru a babban masallacin Zariya da ke jihar Kaduna, zuciyata na mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata sakamakon rushewar masallacin Zariya.
“Ina kuma mika ta’aziyyata ga Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli, da daukacin al’ummar musulmi bisa wannan rashi. Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa wadanda suka rasu.
“Gwamnatin jihar Kaduna za ta taimaka wa wadanda wannan lamari ya rutsa da su,” in ji shi.
Har ila yau, babban sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, a wata sanarwa da ya fitar ya yi kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin aukuwar wannan mummunan lamari.
Hakazalika, a sakon ta’aziyyarsa, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbass, ya bayyana wannan mummunan lamari a matsayin abin takaici da ban tausayi.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi ya rabawa manema labarai, shugaban majalisar ya ce “zuciyarsa na alhinin faruwar lamarin, inda ya ce wannan shi ne labari mai ratsa zuciya da ya samu a ‘yan kwanakin nan.
Abbas, wanda ya bayyana alhininsa, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.