Masana Da Shugabannin ‘Yan Kasuwa Sun Ce BRI Ta Bunkasa Cigaban Duniya

Daga CRI Hausa,

A muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron da ya gudana kwanan baya kan shawarar “ziri daya da hanya daya,” (BRI), ya zayyana alkiblar inganta hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kamar yadda masana da shugabannin ‘yan kasuwar kasa da kasa suka bayyana.

Haka zalika, sun kuma amince da shawarar BRI a matsayin hanyar bunkasa cigaban duniya na bai daya, kana hanyar dake amfanawa al’ummun kasa da kasa.

Farfesa Sheriff Ghali, shehun malami a tsangayar nazarin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja, a Najeriya, ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya,” ta kasance a matsayin wani dandalin hadin gwiwar kasa da kasa mafi samun karbuwa, kuma tana cigaba da taimakawa kasashen Afrika wajen inganta kayayyakin more rayuwa, da suka hada da fannin sufuri da lantarki.

Diaa Helmy, sakatare janar ta majalisar bunkasa cinikayya ta Sin da Masar dake da ofishinta a birnin Alkahira, ya ce, shawarar BRI ta kara tabbatar da samun nasarori da kuma bayar da gagarumar gudummawa a shekaru da dama da suka gabata wajen bunkasa cigaba, da zamanantar da tattalin arziki, da bunaksa kayayyakin more rayuwa a kasashe da dama dake karkashin shawarar.

Helmy tace, gudunmawar BRI ya kara tabbatarwa a bayyane cewa shawara ce da aka gina ta bisa hadin gwiwa, da yin cudanyar moriyar juna dake shafar dukkan bangarori. (Ahmad)

Exit mobile version