• English
  • Business News
Sunday, June 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 weeks ago
in Nazari
0
haraji
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ana kara nuna damuwa game da karuwar ayyukan siyasa, yayin da magoya bayan ‘yan takara ke bayyana maitarsu a fili wajen tallata gwanayensu a babban zaben kasar da zai gudana a 2027, wanda hakan na iya kawo cikas.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, magoya ‘yan takarar na kara kaimin yi musu kamfen a bainar duk da cewa lokacin da aka amince da yin hakan ya rage kusan shekaru biyu.

  • Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi
  • Amfani Da Karfin Gwamnati Kan ‘Yan Adawa Zai Jawo Wa Tinubu Illa A 2027 – Sule Lamido

A dokar zabe Sashe na 94 (1) na 2022 ya bayyana cewa kowace jam’iyyar siyasa za ta fara yakin neman zabe ne kwanaki 150 kafin ranar zabe sannan a kare sa’o’i 24 kafin wannan ranar.

Don haka, wadannan al’amura na ‘yan siyasa na iya yin karan tsaye ga sashe na 94 na Dokar Zaben da aka yi wa gyara a 2014.

Duk da cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa dokar zabe ta 2022 ba ta haramta wa ‘yan takara musamman na daidaikun jama’a da kungiyoyi ba, amma hukumar ta amince da cewa akwai takunkumi kan yakin neman zabe har sai kwanakin sun rage 150 kafin ranar zabe.

Labarai Masu Nasaba

Shirin Fim Kan Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Kan Turbar Dimokuradiyya: Tasiri Da Muhimmanci

Asalin Tushen Matsalolinmu A Nijeriya

A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce wata jam’iyyar siyasa ta fara yakin neman zaben 2027.”

Sai dai wasu lauyoyin da suka zanta da LEADERSHIP sun ce amincewa da ‘yan takara ba magana ce da za a ayyana a matsayin kamfe ba.

A cewarsu, cin zarafin dokar zabe ne kowa ya fara yakinn neman zabe a yanzu.

A nasa jawabin, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da rashin bin doka da oda da ‘yan siyasa ke da shi.

Shittu ya ce, “Batun ba wai na ita kanta doka ba ce, kawai a aiwatar da ita, sashe na 94 na dokar zabe ya fito karara kuma babu shakka, amma ‘yan siyasa da alama suna bin ka’idojin da suka kafa ne kawai.

“Abin takaici ne yadda ake yin watsi da dokokinmu, musamman a tsakanin ’yan siyasa, maimakon a kiyaye su, dole ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara sanya ido tare da hukunta masu karya doka don ya zama an hana.”

Babban Lauyan Nijeriya, Abdul Balogun, ya ce ana sa ran ‘yan siyasa su san ka’idojin: ba za a fara yakinn neman zabe ba sai ya rage kwanaki 150 kafin zaben.

“Zaben 2027 ya rage kusan shekaru biyu, to me ya kowa tattauna batun yakin neman zabe a yanzu? Lokacin da aka amince da da hakan bai zo ba, abin da kuke gani yana faruwa a yanzu kokari ne na kawai daidaitawa, ‘yan siyasa sun san ba za su iya fara kowane irin yakin neman zabe ba tukuna,” in ji shi.

Wani Lauya masanin tsarin mulki Barista Samaila Abu ya zargi ‘yan siyasa da karkatar da robmon dimokuradiyya daga wadanda suka zabe su.

A cewarsa, ‘yan Nijeriya ba su amfana da komai daga ‘ yan siyayar ba tun bayan hawan su karagar mulki a shekarar 2023, amma duk da haka sun fara tattaunawa kan 2027.

“Shin hakan na nufin kwace mulki ne wanda shi ne abin da shugabanninmu suka damu da shi? Da na yi tunanin cewa, da a ce a yanzu jama’a sun amfana daga ‘yan takarar da suka zaba a 2023. To da hakan iya zama rashin abin nuna damuwa, kuma ya zama abu ne da ‘yan siyasa za su daidaita tare da kulla dangantaka kafin kowane zabe; wannan ba zai zama ana nufin yakin neman zabe ba,” in ji shi.

A nasa tsokaci, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da halayyar rashin bin doka da oda da ’yan siyasa ke nunawa wajen kin bin doka da oda.

Don haka, rusassun shugabannin matasan jam’iyyar Congress for Progressibe Change (CPC) da shugaban yankin Neja-Delta, Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, sun yi fatali da tikitin takarar Tinubu/Shettima na zaben 2027.

Shugabannin matasan jam’iyyar CPC na jihar, daya daga cikin jam’iyyun da suka kafa jam’iyyar APC, sun yi kira ga jiga-jigan ‘mambobin da su mara wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima baya kafin shekarar 2027.

Shugabannin matasan CPC Nna kasa sun cimma wannan matsaya ne a karshen taron da suka yi a karshen mako a Abuja domin tattauna makomar jam’iyyar APC da kasa baki daya.

Shugaban matasan Jihar Kogi Sani Ogu Salisu, shugaban rusasshiyar kungiyar shugabannin matasan jihar ta CPC, da sakataren kungiyar Iyke Uwakwe ne suka bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

Sun yi kira ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jam’iyyar CPC da su goyi bayan tattaunawar masu ruwa da tsaki a karkashin jagorancin Sanata Tanko Al-Makura kan sake fasalin jam’iyyar APC.

Shugabannin matasan CPC sun bukaci shugaban majalisar wakilai Hon. Abbas Tajudeen, Gwamna Umar Bago na Jihar Neja, Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina, da ‘yan Majalisar Dokoki na kasa da na jiha, da kuma jiga-jigan zababbun shugabannin kananan hukumomin CPC na goyon bayan Tinubu/Shettima da masu ruwa da tsaki a karkashin Al-Makura.

“Ku hada hannu da masu ruwa da tsaki a karkashin jagorancin Al-Makura domin sake dawo da martabar jam’iyyarmu don kare kalubalen da ke gabanmu, su kyale jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima gabanin zaben 2027.

“Wannan tallafin yana da matukar muhimmanci ga hadin kan jam’iyya, kokarin sake fasalin zai inganta dimokuradiyyar cikin gida, hadin kai, da zaman lafiya a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya, hadin kai da tsari mai kyau zai kara mana damar samun nasara a zaben 2027. Ta hanyar goyon bayan gwamnatin Tinubu/Shettima, za mu iya tabbatar da ci gaba a ayyukan ci gaban kasa.

“Mun yi imanin cewa aiki tare da goyon bayan tattaunawar masu ruwa da tsaki a karkashin Al-Makura zai karfafa jam’iyyarmu da kuma ba mu damar samun nasarar zabe.

“Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da mu domin gina jam’iyyar APC mai karfi da kuma kyakkyawar makoma ga Nijeriya,” in ji su, inda suka kara da cewa shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Hon. Abubakar Maikudi, da su koma jihohinsu daban-daban da kuma hada kan jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Hakazalika, Tompolo ya nuna goyon bayansa ga sake zaben Shugaban Kasa Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise News a ranar Asabar, Ibe-Ebidouwei na Ijaw Nation kuma Grand Patron na PBAT Door-2-Door Mobement 2027, ya bayyana Tinubu a matsayin gogaggen shugaba da gogewa wajen daukaka Nijeriya zuwa ga mafi girma.

Tompolo ya ce “Tinubu mutum ne nagari, yana da gogewa wajen yin komai da kuma kai kasar nan zuwa wani mataki mai girma.”

Ya jaddada cewa, ya kamata a mutunta wa’adin shekaru hudu na Tinubu, tare da yiwuwar sake tsayawa takara na wasu shekaru hudu, inda ya kwatanta wa’adin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas. “Ba ma son kowa ya kawo matsala, a bar shi ya kammala wa’adinsa na kundin tsarin mulkin kasar guda biyu, sannan za mu kada kuri’a ga wani ya karbi mulki a 2031,” in ji shi.

Tompolo ya bayyana shirin fara yakin neman zabe a fadin kasar, ciki har da ziyarar jihohin arewa, domin samun goyon bayan Tinubu a wa’adi na biyu.

“Za mu yi namu bangaren, har ma mu fita daga kan iyakokinmu zuwa yankin arewacin Nijeriya mu tattauna da ’yan’uwanmu domin ya samu wa’adi na biyu,” in ji shi.

Ya kuma yi nuni da cewa sarakunan gargajiya a fadin yankuna sun amince da yunkurin sake tsayawa takara da Tinubu ya yi, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa goyon bayan da ake samu zai tabbatar da ci gaba da shugabancin shugaban kasa.

Da yake jawabi game da damuwa kan yiwuwar tashin hankali, Tompolo ya yi watsi da ikirarin duk wata kungiya da ke da “tashin hankali,” yana kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su goyi bayan gwamnatin Tinubu.

“Muna kira ga kowa da kowa, kuma da yardar Allah kowa zai tallafa mana,” in ji shi.

Da yake tsokaci kan al’amuran siyasa a Jihar Ribas, Tompolo ya bayyana kwarin gwiwar warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike.

“Zababben gwamnan Jihar Ribas zai dawo,” in ji shi, yana mai nuni da dawowar Fubara kan mukaminsa.

Tompolo ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai je Abuja domin ganawa da shugaba Tinubu da Wike domin magance matsalolin da ke addabar Jihar Ribas.

“Shugaban mu ya dade yana kare dimokuradiyya, babu yadda zai yi ya durkusar da ita,” in ji shi.

Kalaman fitaccen dan kabilar Ijaw na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara tabarbarewa yayin da Nijeriya ke kara fuskantar babban zaben 2027.

Tompolo babban mai ba da shawara ne ga ci gaba da jagorancin Tinubu da kwanciyar hankali a Jihar Ribas.

 

Lokaci ne da mulki zai koma arewa ta tsakiya – Gamayyar kungiyoyin siyasa

Kungiyar North Central Renaissance Mobement (NCRM), gamayyar kungiyoyin da ke jagorantar yunkurin neman shugabancin kasar zuwa yankin siyasa, ta bayyana cewa 2027 lokaci ne da shugabanci zai dawo yankin.

Sai dai gwamnonin yankin da shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya da kuma gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule suka wakilta, sun bukaci kungiyar da ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ladabi, da’a, da kuma nutsuwa.

Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da gamayyar kungiyoyin karkashin jagorancin Farfesa K’tso Nghargbu, suka gudanar da taron tuntuba da shi domin neman goyon bayansa kan dawo da shugabancin yankin.

Ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da bin doka da oda na sake farfado da yankin da ba ta taba samar da zababben shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ta hanyar dimokradiyya ba, domin samun goyon bayan da ake bukata.

Gwamnan da wasu fitattun mutane sun bayyana gamsuwarsu da irin kimar mutanen da Nghargbu ke jagoranta na ganin an amince da yankin Arewa ta Tsakiya, dangane da sauran shiyyoyin siyasar kasa da ke da karfin ikon kasar tun bayan samun ‘yancin kai.

NCRM ta kuma yi shawarwari daban-daban da tsofaffin ‘yan majalisar dokokin kasar da suka hada da Sanata Solomon Ewuga, Sanata Suleiman Asonya Adokwe, da mataimakin shugaban majalisar sarakuna da sarakunan Jihar Nasarawa, Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa.

A yayin ganawar, kungiyar ta nemi goyon baya kan yunkurin da take yi na tabbatar da shugabancin kasa ko mataimakin shugaban kasa a 2027 tare da samun amsoshi masu karfafa gwiwa wadanda suka amince da ajandar Arewa ta tsakiya a daidai lokacin da ya dace.

Har ila yau kungiyar ta gabatar da takardar cimma matsaya ga fitattun ‘yan Nijeriya ciki har da Sarkin Keffi, wanda ya albarkaci dandalin tare da bukata su da su jajirce da sadaukar da kai wajen cimma manufofinsu.

Shugaban kungiyar, Farfesa Nghargbu, ya ce kokarin kungiyar na da nufin sake rubuta tarihin siyasar kasar, wanda a baya-bayan nan ya hana shiyyar Arewa ta tsakiya damar yin takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa a kwanakin baya kungiyar ta bayyana cewa idan har jam’iyyar APC ta zabi bai wa Shugaban Kasa Bola Tinubu ‘yancin kin fara ayyana tikitin takara a 2027, to dole ne abokin takararsa ya fito daga yankin Arewa ta tsakiya, yayin da sauran jam’iyyu za su tsayar da ‘yan takarar shugaban kasa daga shiyyar.

“Bayan tarihin Arewa ta Tsakiya daga manyan ma’aikatun kasa guda biyu ya zarce duk wani ikirari na mayar da siyasa saniyar ware daga kowane yanki na geopolitical. Muna ba da shawara mai karfi cewa bukatun adalci, da hadin kai na siyasa ka iya fara haduwa da jagororin jam’iyyar adawa, PDP, da kuma jam’iyyar APC mai mulki, wajen zaben ‘yan takarar su na shugaban kasa da mataimakinsa a 2027.

“Duk sauran jam’iyyun siyasar da ke da muradin shugabancin kasar nan a cikin shekaru biyu su ma su yi taka-tsan-tsan daga wannan adalcin siyasar da ake sa ran mutanen Arewa ta Tsakiya ke nema, irin wannan mataki a lokaci guda zai biya bukatun duk wani hazikin dan siyasa da ake sa ran kowace jam’iyya da hannunta a kan al’ummar kasa.

“A kan haka ne mu ‘yan Arewa Central Renaissance Mobement (NCRM) muke nema, domin tabbatar da gaskiya, daidaito da adalci, a mika ofishin Shugaban Nijeriya ga Arewa ta Tsakiya a 2027,” in ji ta.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027

Next Post

Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi

Related

Zabe
Nazari

Shirin Fim Kan Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Kan Turbar Dimokuradiyya: Tasiri Da Muhimmanci

2 months ago
Asalin Tushen Matsalolinmu A Nijeriya
Nazari

Asalin Tushen Matsalolinmu A Nijeriya

8 months ago
Sinadarin Ƙara Kuzari Lokacin Jima’i
Nazari

Sinadarin Ƙara Kuzari Lokacin Jima’i

12 months ago
Zabe
Labarai

Farashin Shinkafa, Tumatir Da Gari Ya Qaru Da Kashi 141 Cikin Shekara Guda – NBS

12 months ago
Kwarewar Sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN)
Nazari

Kwarewar Sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN)

2 years ago
Halittar Mata Na Canzawa Bayan Aure
Nazari

Halittar Mata Na Canzawa Bayan Aure

2 years ago
Next Post
Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi

Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma'aikata Albashi

LABARAI MASU NASABA

Wakilin Sin Ya Soki Yadda Amurka Ke Tafiyar Da Kudurin Takunkuman Sudan Ta Kudu

Wakilin Sin Ya Soki Yadda Amurka Ke Tafiyar Da Kudurin Takunkuman Sudan Ta Kudu

May 31, 2025
CMG Ya Watsa Shirin Musamman Na Bikin Duanwu Na 2025

CMG Ya Watsa Shirin Musamman Na Bikin Duanwu Na 2025

May 31, 2025
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

May 31, 2025
Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane

Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane

May 31, 2025
Ministocin Wajen Sin Da Kamaru Sun Gana Kan Alakar Kasashensu Da Batun Kafa IOMed

Ministocin Wajen Sin Da Kamaru Sun Gana Kan Alakar Kasashensu Da Batun Kafa IOMed

May 31, 2025
Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum

Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

May 31, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Unity Cup Bayan Doke Jamaica A Bugun Fenarati

Nijeriya Ta Lashe Gasar Unity Cup Bayan Doke Jamaica A Bugun Fenarati

May 31, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Kasashe Masu Tasowa Ya Dade Da Zama Kan Gaba A Bangaren Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Waje

Hadin Gwiwar Sin Da Kasashe Masu Tasowa Ya Dade Da Zama Kan Gaba A Bangaren Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Waje

May 31, 2025
Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara

Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara

May 31, 2025
Hukumar Shiga Tsakani Za Ta Samar Da Sabbin Damammakin Sulhunta Rikici

Hukumar Shiga Tsakani Za Ta Samar Da Sabbin Damammakin Sulhunta Rikici

May 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.