Ya zuwa karshen shekarar 2024, yawan kamfanonin dake cikin masana’antar mutum-mutumi mai basira a kasar Sin ya kai 451,700, wadanda jimillar jarinsu ta kai yuan tiriliyan 6.44 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 880, kamar yadda hukumar kula da kasuwannin kasar ta bayyana.
Yawan irin wadannan kamfanoni ya karu da kashi 19.39 cikin dari idan aka kwatanta da karshen shekarar 2023, wanda ke nuna daidaito a ci gaban masana’antar a kasar Sin.
- Gaskiya Ta Bayyana Bayan Da Gwamnatin Amurka Ta Sanar Da Rufe USAID
- Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Iyali 3 A Filato
Hukumar ta ce, kusan kashi 80 cikin dari na wadannan kamfanoni sun fi yawa a sassa uku, wato sashen binciken kimiyya da hidimomi na fasaha, da watsa bayanai, da hidimomin manhajoji da fasahar bayanai, da sashen dillanci da sari na kayayyaki.
Yankin gabashin kasar, wanda ke da fa’idoji na musamman da suka dace da yankin, da karfin bincike da ci gaba, da ingantaccen tsarin masana’antu, ya zama cibiyar dake da kusan kashi biyu bisa uku na kamfanonin masana’antar mutum-mutumi mai basira a kasar Sin.
Kana adadin irin wadannan kamfanoni a yankunan tsakiya da arewa maso yammacin kasar Sin ya kai kashi 15.33 cikin dari da kashi 14.97 cikin dari na jimillar kamfanonin bi da bi. (Mohammed Yahaya)