A cikin kwanakin da suka gabata a jere, taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 20 ya janyo hankalin kasa da kasa matuka.
Yayin da aka rufe taron, masanan Afirka sun bayyana cewa, taron yana da babbar ma’ana, wanda zai haifar da babban tasiri ga kasar Sin, har ma zai kara kuzari ga kasashen duniya wajen yin hadin gwiwa don tinkarar kalubale da samun bunkasuwa tare.
Darektan cibiyar nazarin harkokin Sin dake Nijeriya Charles Onunaiju ya yi nuni da cewa, Sin tana son samar da gudummawa ga sauran kasashen duniya wajen samun ci gaba, kana bunkasuwar kasar Sin za ta yi tasiri ga duniya baki daya.
Don haka, yana fatan kasashen duniya za su koyi fasahohi da shirye-shiryen samun ci gaba na kasar Sin da kuma damar hadin gwiwa daga taron wakilan JKS karo na 20, ta yadda za a tafiyar da harkokin duniya da ma tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta tare.
Farfesa Costantinos Berhufesfa na jami’ar Addis Ababa ta kasar Habasha ya yi nuni da cewa, nasarorin da kasar Sin ta cimma a aikin zamanintar da kanta bisa tsarinta, sun karfafa gwiwar kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa, wannan zai baiwa sauran kasashe masu tasowa damar zabar dabarun raya kasashensu dake dacewa da yanayinsu. (Zainab)