Kwamitin Zakka na Masarautar Hadejia a Jihar Jigawa, ya tattara tare da raba zakka da darajarta ta kai fiye da naira biliyan 1.072 ga mabuƙata da ke Masarautar.
A cewar wani rahoton da aka gabatar wa Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar, an raba kuɗaɗen da kayan tallafi ga iyalai 185,000 a faɗin Masarautar a lokacin Zakka na shekarar 2024 zuwa 2025 (1446 AH).
- Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya
- Mutane 6,000 Sun Amfana Da Zakka Ta Miliyan N132 A Masarautar Hadejia – Kakakin Masarautar
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, sakataren kwamitin, Ismaila Barde, ya bayyana cewa an samo Zakkar ne daga gundumomi 27 da ke ƙarƙashin Masarautar, wanda ya kunshi kuɗi da amfanin gona da dabbobi.
Ya kuma bayyana cewa a shekarar 2024 kaɗai, kwamitin ya tattara fiye da naira miliyan 300 a matsayin zakka, inda Guri da Auyo da Jabo, suka samar da kaso mai yawa.
A nashi jawabin yayin da yake yaba ƙoƙarin, Sarkin Hadejia ya ƙarfafa gwuiwar masu ikon bayar da Zakka da su ci gaba da cika wannan wajibcin don tallafa wa mabuƙata a cikin al’umma.
Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp