Khalid Idris Doya" />

‘Masarautun Gargajiya Suna Da Gagarumar Rawar Takawa Ga Ci Gaban Dimokradiyya’

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Arct. Abdu Sule Katagum ya bukaci Masarautun gargajiya da su ci gaba da goyon bayan kyakkyawan shugabanci domin kara wa masu kokari kwarin guiwar gudanar da aiyuka nagartacce domin ci gaban talakawansu, hade da kyautata dimokradiyya.

Mataimakin gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya fara rangadi zuwa ga wasu Sarakunar gargajiya da suke karkashin masarautar Katagum, yana mai shaida cewar masarautu suna da mihimmiyar rawar takawa wajen ci gaban dimokradiyya da tabbatar da shugabanci na kwarai musamman kan tabbatar da zaman lafiya.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi a shirye take wajen samar da kudade da kayyakin aikin da ake bukata wa dukkanin masarautun gargajiya da suke fadin jihar domin samun nasarar sauke nauyin da ke kawukansu.

Ya kara da cewa ya kai ziyarar ne domin nuna godiyarsa ga Sarakunan a bisa goyon bayan da suka bashi a kan mukamin da aka nadasa a kwanan nan na mataimakin gwamnan jihar Bauchi.

Da yake tsokaci Hakimin Katagum Mai Kaba, Alhaji Usman Mahmud Abdullahi ya yaba wa gwamnan jihar Bauchi M.A Abubakar a bisa nada Abdu Katagum a matsayin mataimakin nasa, yana mai cewa idan aka yi la’akari da basira da kwarewar Abdu Katagum hakan nasarace wajen kara gina jihar Bauchi.

A wani labarin makamancin wannan da wakilinmu ya nakalto daga Bauchi kuwa, An bukaci gwamnatin jihar Bauchi ta shimfida hade da gina hanyar da za ta hada da kauyen Bakari, Kafin Larabawa, Gadi da Udibu a karamar hukumar Gamawa domin saukaka matsalar zirga-zirga da jama’an yankin ke fuskanta.

Hakimin Sakuwa, Alhaji Mustapha Abdulkadir shine ya yi wannan kiran a lokacin da ya amshi bakwancin mataimakin gwamnan jihar Bauchi Arct Abdu Sule Katagum a ofishinsa.

Hakimin ya bayyana cewar gina hanyoyi da samar da ababen more rayuwa zai bunkasa aiyukan da za su jawo ci gaban tattalin arzikin da zai kai ga inganta rayuwar al’umman yankin.

Daga bisani ya yaba wa gwamnatin jihar a bisa kokarinta musamman ta fuskacin samar da kayyakin kiwon lafiya da sauransu.

Da yake maida martani kan jawabin na Hakimin, mataimakin gwamnan jihar Bauchi Abdu Sule Katagum ya yi alkawarin mika bukatar ga hukumomin da abun ya shafa domin samar da nasarar daukan matakan da suka dace.

Daga nan ya baya wa sarakunan gargaji a bisa hadin kan da suke baiwa gwamnatin jihar, ya kuma kirayesu da su daure a kan hakan domin ci gaban talakawansu.

Exit mobile version