Masu baje kolin kaya su kimanin 300, daga nahiyoyi biyar ne za su halarci bikin ciniki na kasa da kasa da ya shafi bangaren abinci da abin sha na Yammacin Afirka a wannan shekara, wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Har ila yau, sama da masu baje koli 300 ne za su wakilci kasuwanci daban-daban daga sama da kasashe 50 a wannan baje koli da za a yi ranar 11 ga watan Yuni zuwa 13 na wannan shekara da muke ciki a Cibiyar Landmark da ke Jihar Legas, a Biktoriya Ailan.
- Za A Yi Gaggarumin Taron Bunkasa Noma A Legas
- Da Ɗumi-ɗumi: Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Jihar Legas, Soyannwo Ya Rasu Yana Da Shekara 55
Kasashe tara ne za su samu wuraren baje kolin kayansu, wadanda suka hada da Kasar Turkiyya, Dubai, Chana, Indiya, Amurka, Indonisiya, Itali, Egypt da kuma Tunisiya.
Bugu da kari, manyan tawagogi daga Kasar Dubai, Ingila, Thailand, Ukraine, Ghana, Algeriya, Malesiya, Netherlands da kuma wasu kasashe da dama; za su yi amfani da wannan dama, don tallata sabbin kayayyakinsu a Nijeriya da Afirka ta Yamma tare kuma da haduwa da wasu sabbin abokan huldar kasuwanci.
Yanzu a wannan karo na biyar, Afirka ta Yamma a matsayinta na babbar yanki; ita ce za ta baje kolin abinci da abin sha a wajen wannan babban taro. Kazalika, ana sa ran baki akalla 6,000; za su halarci taro da za a dauki kwanaki uku ana aiwatar da shi.
Har wa yau, Manajan kula da baje kolin Brad Smith ya bayyana cewa, “baje kolin wannan shekara na kara nuni ne da samun karin yawan wadanda za su halarci wannan baje koli da kasashe da kuma karin kayayyaki fiye da kowane lokaci. Sannan, idan kuna neman sabbin kayayyaki masu ban sha’awa; wadanda har yanzu ba ku gani a kasuwannin Yammacin Afirka ba, ko shakka babu ba za a rasa a taron wannan baje koli ba.
“Baje kolin wannan shekara, ya karo yawan kasashen da za su baje kolin kayansu fiye da kowane irin lokaci a baya. Haka zalika, sabbin kayayyakinmu na Kasashen Amurka, Chana da kuma Itali, sunan shiga Kasashen Turkiyya, Dubai, Indiya, Indonisiya da kuma Egypt. Sannan kuma, muna maraba da masu baje koli a karon farko daga kasashe irin su Medico, Koreya, Hong Kong, Oman, Saudiyya, Algeriya, Iran, Libya, Turkmenistan da kuma Nepal”, in ji shi.
Kazalika, taron ya samu natija ne sakamakon yawan kasashen ketare da za su halarce shi, wanda ya yi matukar jan hankalin baki; musamman daga yankunan Afirka ta Yamma da sauran sassan duniya daban-daban.
“Don haka, muna yin alfahari da kanmu; a kan ingancin da muke da shi, wanda ya yi daidai da wanda ake bukata a duniya; wanda shi ne ya ba mu damar yin wannan wakilci.
Haka nan, wannan baje koli ne na musamman; wanda za mu kawo muku nau’ikan kamfanonin abinci da abubuwan sha na duniya zuwa wannan kasa Nijeriya tare da masu baje koli da masu ziyara da kuma dukkanin masu neman yin kasuwanci a yankunan Yammacin Afirka,” in ji Smith.
Daya daga cikin masu baje kolin kasa da kasa, rukunin kamfanin abinci na Dena; shi ne zai dauki nauyin wannan taro na Afirka ta Yamma. Wannan kamfani a Landan yake, sannan mai kamfanin wato, Dena babbar dila ce a bangaren sayar da kayan abinci, ta kuma kware tare da sanin sabbin abubuwan da ake amfani das u wajen sarrafa abincin, kama daga kan mai har zuwa sauran kayan hadi.
Har ila yau, wannan kamfani na ganin manyan damammaki a kasuwannin Nijeriya, lura da karuwar bukatar da ake samu a nan na samar da ingantattun kayayyaki.
“Bugu da kari, wannan baje koli da za a yi a wannan yanki na Afirka ta Yamma, zai yi matukar ba da dama; musamman wajen haduwar manyan kamfanonin abinci na wadannan yankuna na Yammacin Afirka,” in ji Kochhar, Shugaban Kasuwancin kasa da kasa.
“Mun yi imanin cewa, wannan abin aka kudiri niyyar yi; ya yi daidai da namu burin na fadada kasancewarmu a wajen da kuma kasashen da ke makwabtaka da mu. Wannan dalili ne, yasa muke kallon wannan taro a matsayin wani dandamali mai matukar muhimmanci; domin baje kolin abubuwan da muke da su.
“Manufarmu ta farko ita ce, kafa kungiyar abinci ta Dena a matsayin amintacce; sannan kuma wanda zai samar da abinci mai matukar inganci a kasuwannin Afirka.
Haka zalika, muna kuma da shirin kulla hadin gwiwa tare da manyan ‘yan kasuwa, Otel-otel da kuma gidajen sayar da abinci tare da baje kolin manyan nau’ikan kalolin kayayyakin abinci da suka hada da Filawa, Kwai, Man girki, Hatsi da sauran makamantansu.”
Wani daga cikin masu baje kolin na kasa da kasa, wato kamfanin Linc Drinks, shi ma daga Landan; wanda yake samar da lemukan shad a kuma barasa, Manajan wannan kamfani Zoryana Slater, ya yi matukar bayyana farincikinsa na kasancewa a wannan babban taro na baje koli.
“Burinmu shi ne, samar da dabarun hadin gwiwa da samar da hanyoyin baje kolin hajojinmu tare kuma da sanya wa mutane sha’awar kayayyakin da muke dauke das u, don su gani su kuma saya,” a cewar Zoryana Slater.