Daga Ahmed Muhammed Danasabe
Kungiyar Mafarauta ta Najeriya reshen Jihar Kogi (KGHGN) ta kama wasu wadanda a ke zargi da satar jama’a tare da yin garkuwa da su guda biyu, wadanda su ke tare jama’a a kan babban hanyar Lokoja zuwa Okene a safiyar Alhamis da ta gabata.
Kwamandan kungiyar Mafarautan na jihar, Bature Inusa, ne ya jagoranci mafarautan zuwa maboyar masu garkuwa da mutanen biyo bayan samun bayanan sirri da kungiyar ta yi.
Bayan sun yi ma sa tambayoyi ne sai ya amsa da bakinsa cewa shi ke bai wa masu garkuwa da mutanen bayanan yadda za su gudanar da ta’asarsu ta garkuwa da mutane.
Bayan samun bayanan sirri ne, sai Kwamanda Inusa ya jagoranci mafarautan har maboyar masu garkuwa da mutanen, inda su ka samu nasarar kama wani mai suna Suleiman Naru.
Kwamandan ya ce, “a yayin da mu ka yi wa wanda mu ke zargin tambayoyi, ya shaida ma na cewa, dukkansu na zaune ne a Kabba Junction kuma sun yi garkuwa da wata mata, inda su ka karbi kudin fansa Naira miliyan biyar daga ’yan uwanta kafin su sake ta.”
Ya kuma shaida ma na cewa, “shugabansu ya ba shi Naira 120,000, inda ya ce zai yi amfani da sauran kudaden wajen sayo makamai a Kaduna.”
Kwamanda Inusa har ila yau ya ce, masu garkuwa da mutanen su tara ne kuma sun yi garkuwa da mutane uku, ciki har da mai dakin tsohon shugaban karamar hukumar Okene. Kazalika, ya tabbatar da kama mutun guda cikin masu garkuwa da mutanen da kuma mai taimaka musu da bayanai.
Kwamandan kungiyar mafarautan wanda yace nan bada dadewa ba za a mika su ga yan sanda,ya kuma ce mafarautan suna nan suna bin sawun sauran masu garkuwa da jama’ar don damke su, inda yace da yardan Allah sai sun kama su.
Daga nan Inusa ya roki gwamnatin jihar Kogi data samar wa kungiyar mafarautan kayayakin aiki irinsu motocin hawa da ofis ofis da na’urorin sadarwa da kuma dan abin kashewa ga mambobin kungiyar domin kara musu kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
Cikin abubuwan da aka gano daga masu garkuwa da jama’ar sun hada da bindiga kirar AK 47 kirar cikin gida guda daya da kananan bindigogi kirar pistol guda uku da albarusai da kuma kullin ganye da ake zargin tabar wiwi ne.
A yayin hada wannan rehotu, wakilimmu bai kai ga jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandar jihar Kogi, DSP Williams Ayah, a hukumance ba.