Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe ɗaya daga cikin ƴaƴan Janet Galadima, wata alkaliyar kotu, a lokacin da suka yi garkuwa da su a Kaduna.
Masu garkuwa da mutanen na neman a biya su kudin fansa Naira miliyan ₦300m domin sako sauran ƴaƴanta. An yi garkuwa da Alƙaliyar da ƴaƴanta huɗu a gidansu yayin da mijinta Dakta Musa Gimba Dutse ya tafi wani taron a Kano.
An kashe babban ɗan, Victor a ranar 2 ga Yuli, 2024, a wani yunƙuri na matsawa dangin su biya kuɗin fansa.
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke Kano
- Rikicin Masarautar Kano: NNPP Ta Nesanta Kanta Daga Umarnin Kwankwaso Ga Ƴan Majalisa
Da take mayar da martani kan lamarin, shugabar kamfanin House of Justice, Gloria Mabeiam Ballason, ta yi Allah-wadai da garkuwar da aka yi da kuma kisan, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro tare da yin kira da a gaggauta samar da kayan aiki don kubutar da waɗanda aka kama tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Ita ma ƙungiyar likitocin Nijeriya reshen jihar ta nuna rashin jin dadin ta, inda jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Dakta Shu’aibu Joga, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an sako iyalan da kuma magance matsalar sace-sacen mutane a jihar.
Ƙungiyar ta bayyana buƙatar gudanar da taron gaggawa da kuma taron manema labarai domin jan hankalin hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen kubutar da waɗanda lamarin ya rutsa da su da sauran mutanen da aka sace ciki har da wani likita da aka yi garkuwa da su watanni shida da suka wuce. Sun kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da yin taka-tsan-tsan a tsakanin mambobinsu yayin da suke tattaunawa da jami’an tsaro domin tunkarar barazanar da ake fuskanta.