Daga A. A Masagala, Benin
Hajiya Maimuna Abubakar ta nemi daukacin masu hannu da shuni a cikin Nijeriya da su taimaka wa mabukata a cikin irin arzikin da Allah (SWT) ya hore mu su don a samu rage kaifin matsalolin rayuwa, wadanda da dama ‘yan Nijeriya su ke fuskanta.
‘Yar kasuwar Hajiya Maimuna, ta bayyana haka cikin wata hira da Leadarship A Yau a garin Auchi ta Jihar Edo, karshen makon nan, inda ta ce, muna da mawadata da suke da karfin karziki na ciyar da mabukata a kasarnan ba sai tare da hannun gwamnatin kasa ba, amma sai ya kasance rashin imani ya hana masu dukiyar su taimaka.
Saboda haka, “kiran da zan yi mu su ita ce su nemi yardar Allah da irin wannan wadatar da Ubangiji ya yi mu su ta hanyar taimakawa marasa galihu da marayu da nakasassu da musakai da sauran mabukata domin ta wannan taimakawar sai a samu zaman lafiya da mutuntawa tsakaninsu da wadanda suke matalauta.’’