Malamai masu koyar da littafin Allah mai Girma wanda komai na duniya da lahira ya na cikinsa ne kuma shi ne Littafi kwaya daya tak Tilo wanda shi ne littafi mafi girma ga daukacin musulmin duniya ke alfahari da shi wato Alkur
ani mai girma.
Malamai masu koyar da wannan litafi da dalibansu wanda suka sadaukar da rayowarsu wajen koyar da shi ga dalibansu nasu na bukatar tallafin Gwamnatin Tarayya, kamar yadda aka tallafawa malaman makarantun buko masu zaman kansu da Gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari ta yi sakamakon kulle makarantu da akayi na wasu watanni, saboda yaki da cutar Korona da ta mamayi duniya a shekarar 2020.
Wadannan bayanai sun futo ne daga bakin kwamred Murtalla Bala Mai sallah, wanda Shugaba ne a kungiyar Inuwar Yayan Malam ta Gwagwarmayar Neman ‘yanci da walwalar malamai da al`majirai masu karanta latafin Allah a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin kano.
Ya ce, bisa ga la’akari da kundin tsarin mulki na cewa duk dan kasa yana da ‘yancin ya rayu yadda kowane dan kasa ke rayuwa da kuma kulawa da shi kamar yadda ake kulawa da sauran ‘yan kasa, to suma malaman masu karantar da littafin Allah wanda akafi sani da masu koyar da karatin Allo, suma suna yana da kyau Gwamnatin Buhari da Gwamnatocin jihuhi su taimaka masu kamar yadda aka taimakawa masu karatun zamani a makarantu masu zaman kansu da albashin akalla na wata uku wanda Gwamnatin Buhari ta bayar ga Malamai wadanda makarantu masu zaman kansu musamman idan akai laakari da yadda Gwamnatin ke ikirarin tabbatar da daidaito da yiwa ‘yan Nijeriya adalci a tsakanin al
ummar kasar.
A karshe Malam Murtala Bala Mai Sallah, shugaban Inuwar yayan Malam na kasa ya ce burin wannan kunkiya shi ne samar da walwala da yanci ga masu hidima ko neman sani a cikin litafin ubangiji ya kuma shawarci daukacin alumma da kuwane mutum ya sa zuciyar tausayi da taimakon al
uma a zuciyasa domin duk abunda ka shuka shi ne zaka girba a gobe.