Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC na Jihar Kano sun kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne a Kano.
Kakakin rundunar, Ibrahim Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge a jihar.
- Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Ranar Juma’a —Hadi Sirika
- Kwana 4 Ga Rantsuwa: Yadda Shugabannin Duniya Ke Tururuwar Rantsar Da Tinubu
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin su ne Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 da Abdullahi Bashir mai shekaru 25 da Ahmed Ibrahim mai shekaru 21 da kuma Zulkifil Bello mai shekaru 25.
Sanarwar ta bayyana cewa, “Sun kasance suna gudanar da ayyukan ta’addanci a kusa da Sabon Gari, cikin karamar hukumar Fagge inda suke kwace wayoyin hannu na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.”
Kakakin ya bayyana cewa jami’an hukumar leken asiri ne suka gano barayin.
Rundunar, a cewar sanarwar, ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da ‘yantar da jihar daga duk wani nau’in aikata laifuka.
Ta koka da cewa a baya-bayan nan ana kara samun karuwar matsalar kwace da sace-sacen wayar jama’a a cikin birnin Kano tare da tabbatar da aniyar ta na dakile wannan lamari.
Ya bayyana cewa, a ranar Talata wasu fusatattun mazauna garin suka kone babur mai uku da ake zargin wasu masu kwace waya ke amfani da shi wajen kwace wayar mutane.