Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce, wasu da suka kasance masu aikata manyan laifuka da suka kware a dabanci su 222 sun tuba kuma tuni suka mika wuya tare da ajiye makamansu.
Kazalika, wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban su 98 sun shiga hannun rundunar a watan Satumba.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4, Sun Raunata 5 A Kaduna
- Mutane Miliyan 826 Sun Yi Yawon Shakatawa A Yayin Ranaikun Hutu Na Kasar Sin
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan jiya, inda ya kara da cewa, rundunar ta yi amfani da dabaru wajen shawo kan matsalolin ta’addanci a jihar.
Kiyawa, ya kara da cewa wadanda suka ki tuba suka daina aikata laifuka sun fada tarkonsu, kuma wasu sun tsere su bar garin.
Yana mai karawa da cewa, wadanda suka tuba suka mika wuyar yanzu haka suna aikin taimaka wa ‘yansanda domin kyautata zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaban tattalin arziki da bunkasar ci gaban jihar.
Ya kara da cewa, wadanda aka kama bisa zarge-zargen daban-daban sun hada da, mutum 28 da ake zargi da fashi da makami, takwas kuma ana zargin su da garkuwa da mutane, biyar kuma ana tuhumar su da kasancewa dillalan miyagun kwayoyi, 176 barayin motoci, uku barayin Adaidaita Sahu, takwas barayin babura, 17 ana zargin su da dabanci da kuma uku da ake zargin su da aikaga damfara.
A lokacin da yake yaba wa jami’an ‘yansandan rundunar bisa nuna kwarewa da gudanar da ayyukansu yadda ya dace, kwamishinan ‘yansandan jihar, ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa hadin kai da suke ba su.
Ya kuma ya roke da su kara ba su hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.