Duk da dokar hana fita ta awanni 24 da gwamnatin jihar Jigawa ta sa, wasu ɗaruruwan matasa sun ci gaba da yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a karo na biyu a wasu sassan birnin jihar Dutse.
Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin shawo kan masu zanga-zangar, musamman a yankin Zai, inda ƙoƙarin hana matasan shiga yankunan kasuwanci da manyan gine-gine suka ci tura. Masu zanga-zangar suna rera waƙoƙin masu suka ga gwamnati kuma sun ƙi warwatsewa duk da harba hayaki mai sa hawaye.
- Masu Zanga-Zanga Sun Ƙona Ofisoshin Ƴansanda, Sun Kashe Babban Jami’i
- Barazanar Zanga-Zangar Kuncin Rayuwa Ta Girgiza Nijeriya
A wajen Dutse, musamman a Shuwarin, dubban matasa sun sake haɗuwa suna ci gaba da zanga-zangar. Jami’an tsaro sun kafa shingaye don hana shiga babban birnin jihar kuma sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa dandazon. Shaidu gani da ido sun ba da rahoton kama wasu matasa da kuma ƙananan yara maza da Ƴansanda suka yi.
A garin Gumel, al’amura sun kasance cikin kwanciyar hankali yayin da jami’an tsaro suka rufe manyan tituna don hana masu zanga-zangar sake haɗuwa. Duk da haka, yanayin yana nuni da cewa adadin jami’an tsaron da ake da su a ƙasa ka iya zama bai wadata ba don tabbatar da tsaro na dogon lokaci.