Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan fili mai albarka na MARURUN ZUCIYA, shafin dake zakulo muku matsaloli da kuma hanyar da za a magance matsalar.
- Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato
- KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan ÆŠaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano
A wannan lokacin zan dan yi tsokaci wato jan hankali, ko na ce dan fadakarwa, har ma da tunatarwa, musamman a kan matan da suke da aure, wadanda ba su jima ba.
Wani abun mamaki a kasar hausa ko na ce a Arewacin Najeriya wai bazawara ce take yawon yin tallan maganin mallakar miji to, saboda Allah mene ya sa ita ba ta mallake nata mijin ta zauna ba?
Mu kula, mu lura, mu kiyaye, su ma mazaje su rika jan kunnen matansu a kan irin wadannan matan. Ko kuma za a yi miki kishiya wata ta dauko kafa ta zo wai tana da maganin da za ki mallake kishiya ko miji sai abin da ki ka ce, karshenta kuma bazawara ce.
Mafi akasarin matan da suke irin wannan tallace-tallacen magungunan zawarawa ne, shin ita ba ta yi amfani da maganin bane ta mallake mijinta ta kasa fita daga gidan miji?.
Mu kiyaye, kuma mu ji taoron Allah, ke da aka kawo wa tallan maganin ki sani babu wani magani da zai sa ki mallake mijinki, tamkar ladabi da biyayya, da bin umarnin Allah subhanahu wa ta’ala. Ki bi mijinki sau da kafa ki yi masa biyayya da ladabi, in ki ka bi Allah ki ka bi manzon Allah (s.a.w), ki ka kyautatawa mijinki ai kin mallake miji, me miji yake da bukata?, kar ki yarda wani ko wata ya kawo miki wani magani ya ce ki yi amfani da shi na mallake miji, ai kyakkyawan maganin mallakar miji ga ‘ya’ya mata shi ne; ni-na-yi-bari -na-bari, ayi biyayyar aure, kuma babu wata biyayya da Manzon Allah (s.a.w) bai fade ta a hadisi da za a bi ba a zauna da maza lafiya.
Kuma masu yaho suna sayar da magungunan kuna cewa maganin mallake miji ko a hana kishiya shigowa a ji tsoron Allah, ku sani idan mata ne ku kun girma kun haifa ‘ya’yanku za su yi aure a wani gidan, idan ma baku haifa ba to, ku sani kannenku ko ‘yan’uwanku za su yi aure a wani gidan, abin da ka je ka yi wa ‘yar wani ka hana ta zaman gidan miji to, kai ma tana nan kamar sako ne ka bayar.
Idan wata matsala ki ke ciki tsakaninki da mijinki ina mai baki shawara addu’a ita ce maganin komai, domin garkuwa ce kuma takobi ce ga mumini, ba wani abu da addu’a ba za ta yanka shi ba, babu wani abu da addu’a ba za ta kare ka da shi ba.Â
Ki yi addu’a ki gayawa Allah (s.w), ki samu mijinki ke da shi ku yi magana da shi, ko shaidan ne mijinki idan ki ka kwantar da kai, ki ka yarda shi uba ne a gare ki, ki ka yi masa biyayya, ki ka yi masa ladabi, ki ka bi ta sanyin murya ki ka yi masa magana, in wani abu ne za ku sasanta tsakaninku, ba sai an tayaki da maganin mallakar miji ba.
Maganin mallakar miji har sai an baki labari?, ubangiji Allah ya zaunar da matan mu lafiya, da kannenmu da yayyenmu dukkaninsu Allah ya kara musu lafiya, wadanda ba su da miji ubangiji Allah ya mallaka musu, zawarawan ma da suke yaho suke irin wadanan barnace-barnacen son kai, da son zuciya da neman kudi, ubangiji Allah ya basu miji nagari kuma Allah ya shirye su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp