Abubakar Abba" />

Mata Masu Bugun Mazajensu Na karuwa A Legas

Kwamishinan Shari’a na jihar Adeniji Kazeem ya fasa kwai, inda ya ce ana samun rahotanni karuwar matan aure da ke yi wa mazajensu dukan tsiya a fadin jihar.Acewar kwamishinan, kimanin matan aure 138 da suke zaune a jihar Legas aka gurfanar dasu a gaban Kotu saboda jibgar mazan su na aure.Kwamishinan ya sanar da hakan ne lokacin da yake bayani akan nasarar da ma’aikatar sa ta samu a shekarar da ta gabata.Adeniji ya sanar da cewar, karar da maza ke shigarwa a kotu kan yadda mata ke lakada musu duka ta haura ta wadda matan ke kai maza yawa Yaci gaba da cewa, kimanin mata su 138 aka samu hannuwan su dumu-dumu a cikin cin zarafin mazajen su.Kwamishinan ya kuma bayyana cewar, har zuwa yau, sashen kula da cin zarafin ‘yan adama na jihar, ya karbi jimillar kara har guda 138 a kan cin zarafin mazan aure.Ba wannan ne karon farko da ake samun matan da ke cin zarafin mazajensu na aure ba. Idan za a iya tunawa a ranar 19 ga watan Nuwambar 2017, an ruwaito labarin marigayi Billayaminu Bello Halliru wanda mai dakin sa Maryam Sanda ta caka masa wuka bayan da ta samu sakon kar ta kwana a cikin wayar sa da wata mata ta tura masa. Duniya juyi-juyi, kowa yasani cewar maza su ne kan gida. Amma sai dai, lamarin a wannan karnin sai faman canzawa yake inda a wasu sassan kasar nan musaman hakan ya sa ake kiran wasu mijin hajiya ko kuma mijin ta ce.Irin wannan lamarin a jihar Legas sai kara kamari yake, inda wasu mazan auren suke shan na jiki a hannun matan su na aure.

Exit mobile version