• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mata Na Da Jan Aikin Sanin Muhimmancin Kansu Ta Kowane Fanni – Farida Abubakar

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
mata

Duk da wayewar kai da ake ganin al’umma ta samu a wannan karne na 21, har yanzu ana ganin akwai kalubale mai yawa da matan arewa ke fuskanta game da sanin kansu da kuma yadda za su bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma. SHAFIN ADON GARI ya tattauna da tsohuwar shugabar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Jihar Kaduna, HAJIYA FARIDA ABUBAKAR wacce ta yi aiki a matakai na yada labarai daban-daban ciki har da zama sakatariyar yada labarai ta Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, kana a yanzu ta kafa gidauniyar taimakon al’umma mai suna ‘Amana Hope And Care Initiatibes’. Ta warware zare da abawa kan matsalolin mata da dama da yadda za a magance su. Ga tattaunawar kamar yadda ta yi da Editanmu, ABDULRAZAQ YAHUZA JERE kamar haka:

Masu karatu za su so su fara jin da wa muke tare a filinmu na Adon Gari, wannan makon?

Sunana Farida Abubakar Kuma ni ‘yar asalin Jihar Adamawa ce amma girman Jihar Kaduna.

Yaya Takaitaccen tarihinki?

Takaitaccen tarihina, na yi karatun firamare dina a Nuhu Bamalli Primary School da ke Unguwar Sanusi Kaduna a shekarun 1980’s sai Kuma na ci gaba da sakandare a ‘Kueen Amina College’ da ke Kakuri Kaduna, sai na koma gida Adamawa na ci gaba a Aliyu Mustapha Secondary School da ke garin Yola. Bayan na Kammala sai na wuce ‘Federal College of Fisheries and Marine Technology’ da ke Lagos inda na samu Diploma a ‘Fisheries Technology (Kimiyyar Nazarin Kiwon Kifi). Da yake ra’ayina yana kan aikin jarida sai na dawo Unibersity of Abuja inda na ci gaba da karatuna. Na yi aiki da gidan rediyo da talabijin na Jihar Kaduna wato (KSMC) daga inda na ajiye aiki bisa radin kaina a shekara ta 2019.

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko za ki yi wa masu karatu waiwaye game da aikin da kika yi na jarida?

Gaskiya aikin jarida ko wane iri ne, yana burge ni kwarai sai dai kuma na fi kwarewa a Talabijin da rediyo din.

Ta yaya za ki bambance aikin rediyo da talabijin da kuma jarida, sannan wanne ya fi birge ki, kuma me ya sa?

Bambancin radiyo, Talabijin da jarida shi ne ‘reach’ din, shi radiyo ya fi kai ga talaka da kuma dan karkara, Talabijin kuma kana ganin Zahiri amma jarida idan ya wuce shikenan.

Akwai mutanen da suke ganin aikin jarida ba na mata ba ne musamman Hausa/Fulani, me za ki ce?

Aikin jarida na kowa ne, mace ko namiji, ya danganci yadda macen ta dauki kanta.

Akwai ‘yan mata masu tasowa da ke sha’awar yin aikin jarida, wace shawara za ki ba su?

Mata masu tasowa da suke sha’awar aikin jarida, na daya dai su sa himma, na biyu su mutunta kansu don za su hadu da mutane daban-daban a sanadiyyar aikin. Na uku kuma su yi kokarin samun wa iyalansu lokaci a matsayinsu na mata.

mata

Wane abu ne idan kika tuna yake sa ki farin ciki da wanda yake sa ki ciji yatsa idan kika tuna a shugabancin da kika yi na Kungiyar ‘Yan Jarida Mata, reshen Jihar Kaduna (NAWOJ)?

Abin da yake sani farin ciki idan na tuna shi ne a cikin karamin lokaci na aiwatar da wasu abubuwa da wasu ba su yi ba a shekara shida wato (2 terms na shugabancinsu). Shekara daya da wata uku kacal na yi a matsayina na shugabar mata ‘yan jarida na Jihar Kaduna, saboda cikin ikon Allah na fara kenan sai mai girma Gwamnan Jihar Kaduna (Namadi Sambo) na wannan lokacin ya ba ni ‘appointment’  a matsayin Chief Press Secretary na offishin uwargidanshi. Abin da kuma ke sa ni cizon yatsa shi ne, wadanda suka karbi ragama suka rusa abin da na fara na alheri ba tare da sun ci gaba ba.

Kin yi aiki da hulda da jama’a daban-daban, ta wane bangare ne kike ganin har yanzu mata suna da sauran jan aiki a gabansu ta fuskar ci gaba?

Inda na ga mata suna da sauran jan aiki, shi ne wajen sanin muhimmancinsu a kowane fanni, don mace daraja ne da ita kuma a kowane fanni mace tana da rawar da za ta taka na burgewa amma mun kasa gane hakan.

Me za ki ce game da ilimin ‘ya’ya mata a Arewa a wannan zamanin?

Ta fannin ilmi gaskiya yanzu mata na kokari, iyaye sun fahimci amfanin ba ‘ya`yansu mata ilimin addini da na zamani don idan ba ilimin ko rayuwar aure da ta tarbiyyar yara za ta gurbace.

Idan muka koma bangaren zamantakewa, wane abu ne yake ci miki tuwo a kwarya a zaman auren Hausa/Fulani da ya kamata a gyara, bangaren miji da bangaren mata?

Maza su sauke hakkin da ya rataya a kansu a matsayinsu na miji da uba don rashin yin hakan shi ke sa wasu matan wani hali kuma da rashin biyayya ga mazajensu. Gaskiya shi ke ci min tuwo a kwarya.

mata

Kina da kwarewa a fannin aikin gwamnati, ki ba da shawara kan matakin dakile fyade a kasar nan wanda a ganinki zuwa yanzu gwamnati ba ta taba aiki a kai ba?

Matakin dakile fyade, shi ne gwamnati ta dauki tsattsauran mataki a kan masu laifi kuma ta tabbatar da aiwatarwa, in ta yi hakan zai sa a ji tsoron aikata fyaden.

Mun ji kishin-kishin cewa kin kafa Kungiyar Taimakon Al’umma (NGO), yi wa masu karatu cikakken bayani?

Ba kishin-kishin ba ne, na kafa kungiyar taimakon al’umma ne domin in tallafa wa mabukata musanman mata da kananan yara, kuma na kafa kungiyar ce mai suna AMANA HOPE AND CARE INITIATIBES tun 2018.

Me ya sa kika zabi sashen kiwon lafiya don yin aiki a kai?

Na zabi sashen kiwon lafiya ne don mu fadakar da mata hanyar da za su bi wajen neman kiwon lafiya musamman lokacin da suke da ciki, da kuma lokacin haihuwa da kuma kula da abin da aka haifa domin rage mace-macen yara da kuma iyayen, wani lokaci musamman matanmu na karkara.

Mene ne babban burin da kike son cimmawa da wannan kungiyar wanda ko bayan rasuwarki za ki yi farin ciki da shi?

Babban burina shi ne in ga mata musamman talakawa da matan karkara sun samu ingantacen kiwon lafiya da Kuma tallafi da zai amfani rayuwarsu.

Ko akwai wani abu da kike son fada ga masu karatu da ba mu tambaye ki ba?

To kusan komai ma dai na fadi amma ina kara kira ga iyaye da su kara himma wajen bai wa ‘ya`yansu ilmin addini da na zamani domin shi ne gishirin zaman duniya ko bayan ba su zai amfani bayansu. Kuma mata ma su yi kokari su kama sana’a.

Abin da kuma na kusan mancewa ban gaya muku ba, shi ne NGO dina ba harkar kiwon lafiya ta tsaya ba, akwai harkar ilimin, harkar tsangaya, harkar koyar da sana’a (skill ackuisition) da kuma sauransu amma mun fara ne da na kiwon lafiya tukunna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Daliban Makarantar Sakandaren Muscatine Dake Iowa Suka Rubuta Masa

Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Daliban Makarantar Sakandaren Muscatine Dake Iowa Suka Rubuta Masa

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.