Daga Muazu Hardawa, Bauchi
A ci gaba da gudanar da shirin gwamnatin tarayya na ciyar da ɗaliban makarantun firamare a Jihohi 14 na Nigeria, sama da mata dubu ɗaya ke gudanar da wannan aikin a Jihar Bauchi inda suke ciyar da ɗalibai sama da rabin milyan a makarantun firamaren cikin garin Bauchi da yankunan karkarar Jihar.
Me tallafawa gwamna kan wannan shiri, Alhaji Mansur Manu Soro shi ne ya ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilinmu a Bauchi inda ya ƙara da cewa shirin ya samu nasara a tsawon kwanaki goma da aka gudanar da shi kafin hutun da ya gabata, a saboda haka yanzu aka sake ɗaukar Jihar bauchi aka bayar da kuɗin kwanaki 20 don wannan aiki, alhali wasu Jihohin na kwanaki goma aka basu, amma saboda yadda aka samu nasarar wannan aiki a baya da kuma kyawawan bayanai na yadda matan suka gudanar da wannan aiki, ya sa gwamnatin tarayya ta ƙara kima da yawan kwanakin da aka bayar da kuɗi don wannan aiki.
Mansur Manu Soro ya ƙara da cewa tun kafin a fara shirin gwamna ya bashi amanar tsara yadda shirin zai gudana a Bauchi kuma ya tsara ta yadda aka samu nasara, illa yan ƙorafe-ƙorafe da ba za a rasa ba wanda al’adace ta ɗan adam. Amma wannan shiri ya temaka sosai wajen ba yara abinci kyauta musamman ga ɗaliban ƙananan azuzuwa, kuma yanzu suna ƙoƙarin yadda za a faɗaɗa wannan shiri har zuwa kan sauran ɗalibai a kowace makaranta. Don haka ya buƙaci masu gudanar da wannan shiri su ci gaba da riƙe gaskiya don a samu nasara wajen faɗaɗa shirin.