He Lifeng, mataimakin firaministan kasar Sin kuma jagoran kasar Sin kan harkokin tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka, ya gana da tawagar kasar Amurka ta rukunin ayyukan hada-hadar kudi na Sin da Amurka a ranar Juma’a, a nan birnin Beijing.
Ya yi nuni da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Amurka wajen aiwatar da muhimman matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron San Fransisco, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa kyakkyawar alkibla kuma mai dorewa.
- Sin Ta Kasance A Kan Gaba A Duniya A Fannin Raya Makamashi Mai Tsabta
- Mahalartan WEF: Sin Muhimmiyar Injin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa
Ya yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin amfani da tsarin rukunin ayyukan hada-hadar kudi, da tara sakamako da kuma karfafa hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudi.
Rukunin ayyukan hada-hadar kudi na Sin da Amurka wata hanya ce ta musayar harkokin kudi da kasashen biyu suka kafa karkashin jagorancin shugabannin kula da harkokin tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka daga bangarorin biyu, domin aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron da suka yi a Bali. (Yahaya)