Mataimakiya ta musamman kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kaduna, Rachael Averik, ta tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe ta a Kudancin Kaduna.
Rachael tana cikin koshin lafiya, amma direbanta da ‘yarsanda sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.
- Durƙushewar Masana’antu: An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Ƙarshen Matsalar Wutar Lantarki
- Manyan Batutuwa 10 Da Suka Mamaye Siyasar Nijeriya A 2024
Da take bayyana lamarin, Rachel ta ce an kai harin ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025, a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a kan hanyarta ta zuwa Gwantu bayan ta ziyarci masarautar Arak domin ziyarar jaje tare da kaddamar da wani asibiti da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina.
Ta bayyana cewa, daya daga cikin jami’ar ‘yansandan da ke tare da ita da direban motarta sun samu raunuka a artabu da maharan, wanda suka bude wuta kan motar da suke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp